Kotun Koli ta tabbatar da zaben gwamnonin Sakkwato, Taraba da Ribas

Kotun Kolin ta yi watsi da daukaka karar da ke kalubalantar zaben Fubara da Kefas Agbu

Kotun Koli ta tabbatar da zaben gwamnonin Sakkwato, Taraba da Ribas

Hoto: Sanusi Bature

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Aliyu Ahmad na Jihar Sakkwato da Kefas Agbu na Taraba da kuma Simi Fubara na Ribas.

A hukuncin kotun, wanda Mai shari’a Tijani Abubakar ya karanta, ya yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Saidu Umar suka shigar na kalubalantar nasarar zaben Gwamna Ahmed Aliyu.

Kwamitin alkalin ya tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke na cewa PDP ta kasa tabbatar da zargin magudi da rashin bin dokar zabe ta 2022.

Kafin nan sai da Kotun kolin ta tabbatar da Kefas Agbu a matsayin zabebban Gwamnan jihar Taraba.

A zamanta na ranar Alhamis, kotun da kuma tabbatar da zaben Simi Fubara a matsayin Gwamnan Jihar Ribas.

A hukunin da kwamitin alkalai biyar na kotun da Mai Shari’a Ibrahim Saulawa ya karanta, Kotun Kolin ta yi watsi da daukaka karar da dan takarar Gwamnan Ribas na Jam’iyyar APC, Tonye Cole, ya yi saboda rashin hujjoji.

Haka kuma, hukuncin shari’ar Gwamnan Taraba da Mai shari’a Mohammed Lawal Garba ya karanta, ya yi watsi da karar da Jam’iyyar NNPP da dan dakararta na gwamna, Yahaya Sani, saboda rashin dalilai.