Kotun Koli ta yi watsi da bukatar INEC da Gwamnan Ogun a Shari’ar Zabe

Kotun koli ta karbi karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamnan Ogun, Ladi Adebutu, suka daukaka domin kalubalanar nasarar Gwamna Dapo Abiodun.

Kotun Koli ta yi watsi da bukatar INEC da Gwamnan Ogun a Shari’ar Zabe

Kotun Kolin Najeriya (Hoto: Onyekachukwi Obi)

Kotun koli ta karbi karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamnan Ogun, Ladi Adebutu, suka daukaka domin kalubalanar nasarar Gwamna Dapo Abiodun.

Kwamitin alkalai biyar na kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro ya kuma ki sauraron karan da Jam’iyyar APC ta Gwamna Dapo Abiodun da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) suka daukaka daga bisani a kan lamarin.

A yayin zaman na ranar Alhamis, kwamitin alkalan ya sanar da lauyan APC, Wole Olanipekun (SAN) cewa babban karar da aka daukaka a gaban kotun koli ya hade bukatarsu.

Adebutu da PDP suna neman Kotun Koli ta kwace kujerar Gwamna Abiodun, a bisa dalilin saba dokar zabe, magudi da kuma rashin cancantarsa.

Da yake gabatar da jawabinsa, lauyan Adebutu da PDP, Chris Uche (SAN) ya ce ya kamata INEC ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 99 da aka soke zabensu.

PDP da Adebutu suna kuma son Kotun Koli ta soke hukuncin kotun daukaka kara na ranar 23 ga watan Nuwamba, da ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da ke tabbatar da nasarar Gwamna Adiodun.

Amma a martaninsa, lauyan INEC, Abiodun Owonikoko ya bukaci Kotun Kolin ta yi watsi da daukaka PDP da Adebutu.

A hukuncin kotun baya, alkalai biyu sun yi watsi da karar Adebutu da PDP saboda rashin dalili, amma Mai Shari’a Jane Esienanwan Inyang na ganin sabanin haka, inda ta umarci INEC da ta janye takardar shaidar cin zaben da ta ba wa Abiodun, ta da gudanar da sabon zabe a rumfunan 99 da ake takaddama akansu.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda