Kotun Koli: Yau za a san ainihin Gwamnan Kano tsakanin Abba da Gawuna

Kotun Koli za ta sanar da hukunci bayan kawanaki 298 da zaben Gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris, 2023,

Kotun Koli: Yau za a san ainihin Gwamnan Kano tsakanin Abba da Gawuna

A yau Juma’a 12 ga Janairu 2023 ne Kotun Koli za ta yanke hukunci kan zaben Gwamnan Jihar Kano, tsakanin Gwamna Abba Kabir Kano Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP da babban abokin hamayyansa, yi zama Nasir Yusuf Gawuna.

Kotun Koli za ta sanar da hukuncin ne bayan kawanaki 298 da zaben Gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris, 2023, wanda aka shafe sama da makonni 40 ana shari’a a kansa.

Shari’ar dai ta samu asali ne da karar da APC ta shigar gaban Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano tana kalubalantar nasarar Gwamnan Abba, inda take neman a ayyana Gawuna a ma Abba.

Gwamna Abba da NNPP ne suka ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli a wannan shar’a mai cike da rudani ne domin ƙalubalantar ƙwace kujerarsa da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya ta yi.

Suna kuma kalubalantar yi da kuma shirinta na sauya rubutaccen hukuncinta — mai karo da juna — da ya tabbatar masa da kujerar.

Karo na biyu ke nan da gwamnan Kanon ke daukaka kara kan shari’ar, da nufin kare kujerarsa, da kuma rashin gamsuwa da hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano  da  kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya  da suka kwace kujerarsa.

Shari’ar zaɓen dai ta shafe sama da kwanaki 300 tana ɗaukar hankalin jama’a, musamman ma bayan kundin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya kan shari’ar ya fito ɗauke da saɓanin hukuncin da aka karanta a zamanta.

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta gwara kan jama’a

A hukuncin da kotun ta karanta, ta sanar da ƙwace kujerar gwamnan a bisa hujjar cewa shi ba ɗan Jam’iyyar NNPP da ya lashe zaɓe a ƙarƙashin inuwarta ba ne, saboda babu sunansa a rajistar mambobin NNPP da jam’iyyar ta miƙa wa Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC).

Wannan wata sabuwar sarƙaƙiya ce, kasancewar a hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta yanke a watan Satumba, ta bayyana cewa ba ta da hurumi a kan wannan zargin da Jam’iyyar APC ta yi, domin lamari ne na gabanin zaɓe.

Amma Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce kotun farkon ba ta yi aikinta ba, domin kuwa tana da hurumi kan batun halascin takarar Abba a NNPP.

A saboda haka, kotun ɗaukaka ƙarar ta kwace kujerar domin, a cewarta, kujerar ba ta halasta a gare shi ba, domin kuwa INEC ba ta san shi a matsayin ɗan NNPP ba a lokacin zaɓen, don haka ba yadda za a yi ya zama ɗan takarar jami’yyar da shi ba ɗanta ba ne, ballantana ya ci mata zabe.

Sai dai kuma da kotun ta fitar da rubutaccen hukuncin, sai aka ga yana tabbatar da shi Abba a matsayin Gwamnan Kano tare da korar karar APC.

Hakan ya haifar da ruɗani da zargin maƙarƙashiyar neman sauya ainihin hukuncin.

APC na cewa kuskuren rubutu ne, NNPP kuma na cewa gaskiya ta yi bakinta — rubutaccen bayani shi ne abin dogaro — hasali ma, kundin yana ɗauke da sa-hannun magatakarda da alkalan kotun.

Lauyoyi dai sun bayyana cewa akwai tufka da warwara da kuma kura-kurai a rubutaccen hukuncin, lamarin da ya jawo kiraye-kirayen a bincika lamrin, wanda daga baya hukumar kula da shari’a (NJC) ta ce za ta bincika.

Kotun ɗaukaka karar ta bayyana cewa kuskuren rubutu aka samu a kundin hukuncin, amma hakan ba zai sauya hukuncin da ta karanta a zaman da ta yi ba.

Kotun ta kuma bayyana cewa za a iya gyara rubutaccen hukuncin bisa buƙatar bangarorin da abin ya shafa.

Daga baya ta nemi ɓangarorin su dawo da kundin hukuncin da ke hannunsu a gyara.

Amma wasu lauyoyi na bayyana cewa ba ta da hurumin yin hakan, domin lokacin da doka ta ƙayyade mata na sauraron shari’ar ya riga ya wuce.

Hakazalika wasu masana shari’a sun bayyana cewa abin da ke cikin kundin shari’ar ba kuskuren rubutu da aka sani a dokar aikin shari’a ba ne.

Wannan dambarwar dai ta haifar da zanga-zangar magoya bayan Abba da NNPP a Kano, ko da yake ’yan sanda sun hana daga baya.

NNPP da Abba dai sun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli kan hunkuncin kwace kujerar gwamnan da kotunan farko suka yi.

Suna kuma ƙalubalantar hurumin Kotun Daukaka Kara na neman yin sauyi a rubutaccen hukuncin da ya tabbatar wa Abba kujerarsa ta Gwamnan Kano.

A halin da ake ciki wasu lauyoyin sa-kai sama da 200 sun fito za su kare Abba da NNPP a Kotun Koli domin ganin kujerarsa ta tabbata.

A daya ɓangaren kuma lauyoyi kimanin 500 ne suka ce za su kare APC da Gawuna domin ganin Abba Gida-gida ya bar gidan gwamnati ya koma gida.

Hukuncin Kotun farko

A ranar 20 ga Satumba, kotun kotu sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ta kwace kujerar Gwamna Abba bayan ta soke dubu 165 da doriya daga kuri’un da ya samu, a matsayin haramtattu, saboda rashin sa-hannu da hatimin INEC a kansu.

Hakan ya sa Gawuna ya sha gabansa a yawan kuri’u, wanda ya sa kotun ta ayyana Gawunan a matsayin halattaccen wanda ya lashe zaben, ta kuma umarci INEC ta ba shi takardar shaidar cin zabe, ta soke wanda ta ba wa Abba da farko.

Wannan hukunci ne ya sa Abba da NNPP suka garzaya zuwa Kotun Daukaka Kara ta Tarayya domin neman adalci.

Daga nan kuma suka kara daukaka kara zuwa Kotun Ƙoli, wadda suka shaida wa cewa kuri’un da APC ta tantance marasa sa-hannu da sitamfi ba su ma kai 20,000.

Don haka suna kalubalantar soke kuri’un Abba dubu 165, wanda ta ba wa Gawuna damar shan gabansa a wajen aan kuri’u.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a kotun koli.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa