Kotun Koli za ta yanke hukunci kan Zaben Gwamnan Filato ranar Juma’a

Kotun koli ta sanya ranar Juma’a domin yanke hukunci kan rikicin zaben gwamnan Jihar Filato tsakanin PDP da APC

Kotun Koli za ta yanke hukunci kan Zaben Gwamnan Filato ranar Juma’a

Kotun Koli ta sanya ranar Juma’a domin yanke hukunci kan rikicin zaben gwamnan Jihar Filato.

Sakataren yada labarai APC na jihar, Sylvanus Namang, ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Alhamis, inda ya yi kira ga ’yan Jam’iyyar su kwantar da hankalinsu, su bi doka da oda.

A baya dai kotun daukaka kara ta soke hukuncin kotun kararrakin zabe da ta tabbatar da zaben gwamna Caleb Mutfwang na Jam’iyyar PDP, tare da bayyana dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Kotun daukaka kara ta bayyana cewa, takarar Gwamna Mutfwang harmtacciya ce, saboda jam’iyyarsa ta saba umarnin kotuna kan sake gudanar zabukan shugabannin mazabu zuwa matakin jiha.

Sakamakon rashin gwamsuwa da hukuncin kotun daukaka kara ne PDP ta garzaya kotun koli.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji