Kotun Landan ta yanke wa wata ‘yar Ghana hukuncin shekara 8
A ranar Talata da ta gabata ne wata kotu da ke birnin Landan ta yanke hukuncin daurin shekara takwas a kan ‘yar Ghanan nan, wace aka kama ta da hodar ibilis a filin jirgin saman Heathrow bara, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana. Lauyoyin matar sun ce za su tilasta wa kotun […]
A ranar Talata da ta gabata ne wata kotu da ke birnin Landan ta yanke hukuncin daurin shekara takwas a kan ‘yar Ghanan nan, wace aka kama ta da hodar ibilis a filin jirgin saman Heathrow bara, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
Lauyoyin matar sun ce za su tilasta wa kotun Ghana bayyana sunayen mutanen da matar ke taimakawa wajan safarar muyagun kwayoyin. An yanke wa matar mai suna Nayele Ametefe hukuncin ne, bayan kamata da kayi da hodar iblis mai kilo 13 wanda kudinta ya kai fiye Fam miliyan daya da 800 a Landan ranar 9 ga watan Nuwamban bara.
Ametefe dai ta ce manyan ‘yan siyasa da jami’an gwamnatin kasar Ghana ne ke sa ta yi musu wannan aiki tun shekarata 2004. Matar tana kan hanyarta ta zuwa jamhuriyar Dominican ne in da ta tsaya a Landan domin yin sayayya da kuma ganin likita. Har ila yau, a ranar Talata wani babban jigo a jam’iyyar adawar kasar Ghana ta New Patriotic Party (NPP) Mista Dominic Nitiwul ya bayyana a gaban zauren majalisar dokokin kasar da buhun shinkafa mai nauyin kilo 13, inda ya kalubalanci jami’an tsaron kasar da sakaci ta hanyar kwatanta girman buhun da hodar da matar ta fita da ita daga filin jirgin saman Kotoka da ke birnin Accra.