Kotun Masar ta haramta kungiyar Hamas ta Falasdinawa
Wata kotu a kasar Masar ta haramta dukkan ayyukan kungiyar Hamas ta kasar Falasdinu tare da ba da umarnin a kwace ofisoshi da kadarorinta. Wata kara da wani lauya dan kasar Masar ya shigar ya nemi haka bisa zargin alkarta da kungiyar Ikhwanul Muslimina.Gwamnatin sojan Masar ta ayyana kungiyar Ikhwanul Muslimina a matsayin kungiyar ’yan […]
Wata kotu a kasar Masar ta haramta dukkan ayyukan kungiyar Hamas ta kasar Falasdinu tare da ba da umarnin a kwace ofisoshi da kadarorinta.
Wata kara da wani lauya dan kasar Masar ya shigar ya nemi haka bisa zargin alkarta da kungiyar Ikhwanul Muslimina.
Gwamnatin sojan Masar ta ayyana kungiyar Ikhwanul Muslimina a matsayin kungiyar ’yan ta’adda a watan Disamban bara, wata biyar bayan kifar da gwamnatin Shugaba Mohammed Mursi da sojoji suka yi.
Kakakin Hamas, Sami Abu Zuhri ya yi Allah wadai da hukuncin kotun,inda ya ce, “Hukuncin ya zubar da mutuncin Masar da gudunmawar da take bayarwa wajen gwagwarmayar Falasdinawa.”
Ya kara shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa: “Ya nuna wani sabon salon a dakile gwagwarmayar Falasdinawa.”
Ministan Harkokin Wajen Masar Nabil Fahmy ya shaida wa wani taron manema labarai cewa ba ya da masaniya kan hukuncin, sai dai ya kara da cewa: “Duk wanda yake barzana ga zaman lafiyar Masar ya kamata ya fahimci zai hadu da mugun sakamako.”
Manyan jami’an Hamas ciki hard a mataimakin shugaban siyasa Moussa Abu Marzouk suna zaune ne a Masar, kuma suna iya fuskantar barzanar kamawa.
Hamas, wadda take mulkin Zirin Gaza da ke makwabtaka da Masar an kafa ta ne a shekarun 1980, kuma tana da kama da Ikhwanu inda kungiyoyin biyu suke da kyakkyawar alaka.
Tun juyin mulki ga Mursi, mahukuntan Masar suke zargin Hamas da tsoma baki cikin harkokin Masar tare da hada kai da mayaka masu dauke da makamai da ke zaune a Arewacin Tsibirin Sinai wadanda suke kai hare-hare ga gwamnati da jami’an tsaro inda suka kashe daruruwa.
Mursi da wasu mutum 35 suna fuskantar shari’a kan tuhume-tuhumen da suka hada da hadda baki da kungiyoyin kasashen waje – ciki har da Hamas da kuma kungiyar Hizbollah ta ’yan Shi’ar Lebanon da kuma Dakarun Iran domin aikata ta’addanci.
Hamas ta ce wadannan zarge-zarge kirkirarsu aka yi, kuma wani yunkuri ne na bata mata suna.
Tun cikin watan Yulin bara mahukuntan Masar suka takaita zirga-zirga zuwa Rafah iyakar da ke tsakanin kasar da Zirin Gaza tare d lalata daruruwan hanyar karkashin kasa da Falasdinawa ke satar shiga da abinci da makamai da man fetur zuwa kasarsu.