Kotun Musulunci ta rufe gidajen giya biyar a Jigawa
Kotun Lardi ta Shari ar usulinci da ke Kazaure a qarqashin jagorancin Mai shari’a Muhammed Malam Madori ta rufe wasu gidajen da ake zargi na sha da sayar da barasa ne guda biyar na tsawon wata takwas.Mai shari’a Malam Madori ya kuma bai wa ’yan sanda da dogarawan Hisba umarnin kama duk wanda aka gani […]
Kotun Lardi ta Shari ar usulinci da ke Kazaure a qarqashin jagorancin Mai shari’a Muhammed Malam Madori ta rufe wasu gidajen da ake zargi na sha da sayar da barasa ne guda biyar na tsawon wata takwas.
Mai shari’a Malam Madori ya kuma bai wa ’yan sanda da dogarawan Hisba umarnin kama duk wanda aka gani yana qoqarin shiga gidajen da kowane irin dalili ba tare da izinin kotun ba.
Gidajen da aka kulle hudu daga cikinsu suna Unguwar Gadar Kazaure ne, yayin da daya yake Kanti a cikin garin Kazaure.
Alqalin ya yi wa wadanda aka kama a gidajen giyar a lokacin kamen da ’yan Hisba suka yi hukuncin bulala 80 kowannensu tare da tarar Naira dubu bakwai ko kuma bulala 80 da zaman wata biyu a gidan yari.
Shugaban Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa Ustaz Aliyu Muhammad Galamawa ya shaida wa wakilinmu cewa jami’ansa sun kama mutum shida a wata mashaya da ke Sule Tankarkar da ke Masarautar Gumel inda suka gurfanar da su a gaban kotun Musulunci ta Sule Tankarkar aka yanke masu hukuncin bulala 80 da tarar Naira dubu goma kowannesu.
Ya ce kotun shari’ar Musulunci ta Maigatari ma ta yanke hukuncin bulala tamanin ga wasu da ’yan Hisbar suka gurfanar a gabanta bayan ta same su da laifin shan giya a wata mashaya.