Kotun Musulunci ta sa a kamo mawaki Rarara kan ‘boye matar aure’

Mijin matar na zargin Rarara da sanya ta a bidiyon wakarsa ba da izini ba

Kotun Musulunci ta sa a kamo mawaki Rarara kan ‘boye matar aure’

Dauda Kahutu Rarara

Wata kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano, ta bayar da umarnin a kamo sanannan mawakin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara.

Alkalin da ke jagorantar shari’ar, Ibrahim Sarki Yola ne ya bayar da umarnin kamo mawakin saboda kin bayyanarsa a gaban kotu don kare kansa daga zargin da ake yi masa.

Tun da farko kotun ta aike wa Rarara sammaci kan ya bayyana a gabanta ranar 22, ga watan Disambar 2020, saboda tuhumar da ake masa na boye matar aure ba bisa ka’ida ba.

Mijin matar mai suna Abdulkadir Inuwa ne ya shigar da karar yana neman a bi masa hakkinsa a kotun Musuluncin.

Mijin matar na zargin mawaki Rarara da saka matarsa ta aure a bidiyon wakarsa ta siyasa mai taken ‘Jihata, Jihata ce’.

Ya shaida wa kotun cewa an yi wata ba a san inda matar tasa ta shiga ba, don haka ya roki kotun da ta bi masa hakkinsa.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya