Kotun ta umarci dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kazaure ya bayyana a gabanta
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Kazaure bisa jagorancin Alkali Jazuli Rabi’u Ringim ta umarci dan Majalisar Tarayya na yankin masarautar Kazaure, Alhaji Bashir Adamu ya bayyana a gabanta a ranar 25/2/2014 don kare kansa game da kararsa da Alhaji Sadis Abdullahi ya yi kan bata masa suna. Mai shari’a Jazuli ya ce dole dan majalisar […]
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Kazaure bisa jagorancin Alkali Jazuli Rabi’u Ringim ta umarci dan Majalisar Tarayya na yankin masarautar Kazaure, Alhaji Bashir Adamu ya bayyana a gabanta a ranar 25/2/2014 don kare kansa game da kararsa da Alhaji Sadis Abdullahi ya yi kan bata masa suna. Mai shari’a Jazuli ya ce dole dan majalisar ya bayyana a gaban kotun ta ji daga bakinsa sannan za ta iya yanke hukunci. Lauyan da ke kare wanda ake karar Barista Auwalu Iliyasu Magashi ya ce a takardar sammaci da kotun ta rubuta babu abin da ya yi kama da babban laifi, shi ya sa wanda ake karar ya turo lauyansa kawai. Mai shari’a Jazuli ya yi wa wanda ake kara da lauyansa uzirin su kawo takardar sammancin a gaban kotu ranar da za a sake zama domin gamsar da kotun. Alhaji Sadis Abdullahi ya nuna rashin gamsuwa kan yadda wanda ake kara ya ki zuwa kotun, ya ce rashin zuwansa tamkar raini ne ga kotun saboda zama na uku ke nan bai taba zuwa kotun ba. Kotun ta amince da bayanin mai kara, inda ta ce sahi na 36 ya ba wanda yake kara damar cewa dole ne wanda ake kara ya bayyana a gaban kotu koda lauyoyi za su shigo cikin maganar.