Kotun Turai ta cire Hamas daga jerin kungiyoyin ’yan ta’adda
A shekaranjiya Laraba ne wata babban kotun Tarayyar Turai ta cire kungiyar gwagwarmaya ta Hamas daga cikin jerin kungiyoyin ’yan ta’addan duniya. kasashen da dama suna wa kungiyar kallon ta ’yan ta’adda ce, amma mambobinta na bayyana ta da ta kwato wa Falasdinawa ’yanci. Kotun ta dauki matakin ne bayan alkalanta sun duba aikace-aikacen da […]
A shekaranjiya Laraba ne wata babban kotun Tarayyar Turai ta cire kungiyar gwagwarmaya ta Hamas daga cikin jerin kungiyoyin ’yan ta’addan duniya. kasashen da dama suna wa kungiyar kallon ta ’yan ta’adda ce, amma mambobinta na bayyana ta da ta kwato wa Falasdinawa ’yanci.
Kotun ta dauki matakin ne bayan alkalanta sun duba aikace-aikacen da kungiyar take gudanarwa, amma sun dogare ne musamman ga bayanan da aka tattara daga kafofin yada labarai da kuma intanet. Sai dai za a ci gaba da rike kudin kungiyar a asusun da take ajiya a kasashen ketare.
kungiyar Hamas ita ce take da iko da yankin zirin Gaza. Kuma a bana ne mayakanta suka jagoranci yaki da kasar Isra’ila har tsawon kwanaki 50.
Lokacin da yake mayar da martani kan hukuncin, Firaministan kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana Hamas da “kungiyar ’yan ta’adda da ke kisan rayuka” wadda yakamata a mayar da ita jerin kungiyoyi danginta. kasashen Amurka da wasu kasashe da dama sun sanya Hamas a cikin jerin kungiyoyin ’yan ta’adda saboda abin da suka kira a cewarsu kin yin watsi da tada husuma.
An dai kafa kungiyar Hamas ne a shekarar 1987. kungiyar gwagwarmayar ce ta lashe zaben majalisar dokokin Falasdinu a shekarar 2006. Da shekara ta zagayo, Hamas ta kara karfafa ikonta a yankin zirin Gaza bayan ta hanbarar da takwararta wato kungiyar Fatah, wadda a yanzu take iko da yankin Yammacin Kogin Jordan.