Kotun Zaben Gwamna ta kori karar Jam’iyyar ADC a Jihar Gombe

A ci gaba da sauraron shari’ar zabe, Kotun Sauraron kararrakin Zaben Gwamna a ranar Litinin da ta gabata ta kori karar da Jam’iyyar ADC ta shigar inda take kalubalantar nasarar Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo, a zaben da aka gudanar a watan Afirilun bana.Kotun ta kori karar ne bayan ta gano lauyan mai kara Sam Kagbo […]

Kotun Zaben Gwamna ta kori karar Jam’iyyar ADC a Jihar Gombe
Kotun Zaben Gwamna ta kori karar Jam’iyyar ADC a Jihar Gombe

A ci gaba da sauraron shari’ar zabe, Kotun Sauraron kararrakin Zaben Gwamna a ranar Litinin da ta gabata ta kori karar da Jam’iyyar ADC ta shigar inda take kalubalantar nasarar Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo, a zaben da aka gudanar a watan Afirilun bana.
Kotun ta kori karar ne bayan ta gano lauyan mai kara Sam Kagbo ba ya ciki jerin sunayen lauyoyin da za su kare mai kara ko wanda yake kara.
Alkakin Kotun Mai shari’a Mohammad Siraj, a lokacin da yake yanke hukuncin ya ce bisa dogaro da sassa na 1 (2) da na 24 na dokokin shari’a sun nuna cewa sai wanda sunansa ke cikin jerin sunayen lauyoyin da ke gudanar da aikin lauya ne kadai zai iya tsayawa a gaban kotu don kare main kara ko wanda ake kara.
A cewarsa kotun ta kori karar ne saboda sunan Sam Kagbo, lauyan dan takarar Jam’iyyar ADC Ja’afar Abubakar Kwadom, ba ya cikin jerin sunayen lauyoyin Najeriya, don haka ne mai wannan sunan bai cancanci shiga kotu don kare wani kamar yadda tsarin mulkin Nanjeriya a sashi na 36 ya nuna.
Tun farko lauyan wanda ake kara na farko Mista Solomon Umoh Babban Lauya a Najeriya (SAN) ya mika wata takardar roko a gaban kotu inda yake cewa sunan Sam Kagbo wanda lauyan mai karar ya yi amfani da sunan ba daidai yake da sunan Samuel Peter Kagbo da aka
san shi ba.
A hira da manema labarai a wajen kotu jim kadan da yanke hukuncin, lauyan wanda ake karar ya ce hukunci ya yi daidai, duk da cewa mai karar ya ce zai daukaka kara zuwa Kotun daukaka kara kan batun.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista