Kowa da ranarsa
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. Allah Yas a haka amin. A yau na kawo muku labarin ‘kowa da ranarsa’. Labarin ya kunshi yadda wata baiwa ta zama matar sarki. A sha karatu lafiya.A wani gari da ake kira rugga an yi wata mata mai matukar son banza. Duk […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. Allah Yas a haka amin. A yau na kawo muku labarin ‘kowa da ranarsa’. Labarin ya kunshi yadda wata baiwa ta zama matar sarki. A sha karatu lafiya.
A wani gari da ake kira rugga an yi wata mata mai matukar son banza. Duk da cewa Sarkin garin ya sanya doka akan cewa ba ya son kowa ya ajiye wani ko wata a garin a matsayin baiwa ko bawa amma wannan mata sai ta yi kunnen uwar shegu ta cigaba da ajiye bayi a gidanta ba tare da sanin Sarki ba.
Wannan mata da ta ki bin umarnin Sarki ana kiranta Delu, tana da ’ya da ta fi so fiye da komai a duniyar nan. Da ita da ’yarta suka shiga damun baiwarsu da aiki iri-iri. Kamar yin tausa da wanki da girki da sauransu.
Baiwar kullum a cikin bakin ciki take sai kuka. Rannan sarkin garin ya ce yana son yin aure don haka, kowace mace da take garin ta je bakin ruwa da tulu. Hakan ko aka yi. Delu don son banza sai ta aiki baiwar ta wuce mata da tulun bakin rafi don a ganinta kaskanci ne daukar tulu.
Da sarki ya iso sai ya rika bin ’yan matan daya bayan daya yana kallonsu a kokarinsa na zabar matar aure. Can sai ya hango baiwar dauke da tulun ruwa sai ya bukacei ta tsaya don ya sha ruwan da ke cikin tulun amma sai ta nuna masa ba tulunta ba ne. Nan fa Sarki ya ce ai ya samu matar aure, ita kuma baiwar da ta ji haka sai ya koma gidan Delu a guje tana kuka saboda tsoro. Da Sarki ya tambaya sai aka ce ai a gidan Delu take zaune. Nan take Sarki ya aika fadawansa zuwa gidan Delu, ita kuma Delu ta fito da baiwa kuma ta mika wa fadawan Sarki don su kai masa amaryarsa.
Delu cikin bakin ciki ta rungumi baiwar (amaryar Sarki) a matsayin tana taya ta murnar auren Sarkin da ta yi.
Daga nan ne amarya (baiwa) ta sanya Sarki ya gina wa Delu dankararen gida duk da irin rikon sakainar kashin da ta yi mata.