Kowa nawa ne – Buhari

Zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, ya bayar da tabbacin cewa zai rungumi kowa da kowa ba tare da nuna bambanci ba. Ya bayyana haka ne a jawabinsa a ranar Larabar da ta gabata a Abuja, jim kadan da amsar katin shaidar lashe zabe daga hannun Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Attahiru […]

Kowa nawa ne – Buhari

Zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, ya bayar da tabbacin cewa zai rungumi kowa da kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Ya bayyana haka ne a jawabinsa a ranar Larabar da ta gabata a Abuja, jim kadan da amsar katin shaidar lashe zabe daga hannun Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega. “Ni da gwamnatina mai zuwa, mun dauki alwashin gudanar da mulki cikin adalci da sanin ya kamata. Ba zan nuna son kai ko nuna kiyayya ga kowane dan Najeriya ba, saboda kabilanci, jinsi, addini ko bangaranci ko don matsayin mutum ba.” Inji Shugaban mai jiran gado.
A ci gaba da jawabin nasa, ya tabbatar da cewa zai gudanar da gwamnati bisa bin doka da oda, inda ba zai amince da karya doka ba, komai matsayin mutum a cikin al’umma, haka kuma ba zai amince a ci zarafin wani ba, komai rauninsa a cikin al’umma.
Game da harkokin tsaro kuwa, shugaban ya ce zai yi kokarin samar da ingantaccen tsaro, ta yadda al’ummar kasa za su ji dadin zama a gidajensu, kasancewar za a bi kundin tsarin mulki wajen tafiyar da al’amuran kasa bisa dacewa. “Za ku samu bakin magana, ku fadi ra’ayinku ba tare da shayin komai ba, domin babu wanda zai takura maku ko ya ci zarafinku. kaunata da damuwata da wannan kasa zai sa in yi aiki nagari, wanda zai shafi kowa da komai a kasar nan. Aikinmu zai kyautata wa kowa, har ma da wadanda ba su kaunarmu ko siyasarmu. Ku duka nawa ne, don haka zan dauki kowa a matsayin nawa ba tare da bambanci ba. Zan yi aiki don kyautata wa wadanda suka zabe ni da ma wadanda ba su zabe ni ba, da ma wadanda ba su yi zaben ba gaba daya. Dukkanmu muna rayuwa ne da suna daya kuma a karkashin kasa daya. Dukkanmu mu ’yan Najeriya ne.”
A jawabin nasa, wanda ya ja hankalin al’ummar kasar nan da ma duniya baki daya, Janar Buhari ya koma baya, inda ya bayyana cewa, a yayin da yake yakin neman zabe, wasu sun bijiro da bayanai a kansa marasa dadi. A kan haka ya ce duk ma wani abu da yake yi ko ya taba yi, yana yi ne domin hidimarsa ga kasa, saboda kaunarta da kishinta.
“Idan da nuna kasawa wajen cewa ba zan iya shugabanci ba, ba zan taba cusa kaina cikin harkar neman shugabanci ba. A can baya, na yi iyaka kokarina a dukkan ayyukan da na yi wa kasata.” Inji shi.
Game da Shugaban kasa mai barin gado kuwa, Janar Buhari ya ce: “Duk da kacaniya da hauma-haumar yakin neman zabe da suka gudana, ina mika hannun zumunci da sasanci ga Shugaba Jonathan da tawagarsa. Don haka ina bayyana cewa ba ni da wani bakin nufi ko gaba ga kowa.”
Ya kara da cewa: “Bari ma a wannan gaba in tabbatar wa Shugaba Jonathan cewa, bai da wani dalili da zai ji tsoro na. Duk da cewa salon mulkina da nasa ba su zama iri daya ba, amma duk da haka shi dan Najeriya ne mai kima kuma har yanzu shi shugabanmu ne. Yana da bukatar goyon bayanmu kuma yana da bukatar mu ci gaba da girmama shi, musamman ma albarkacin ofishinsa na Shugaban kasa da ya rike. Haka ne kasa mai mutunci ke yi wa shugabanninta da wadanda suka bauta mata, kuma haka ya kamata ma Najeriya ta kasance.”
Game da shirin kafa gwamnatinsa kuwa, Janar Buhari ya ce: “Nan ba da dadewa ba zan gana da Shugaba Jonathan, domin mu tattauna yadda tawagoginmu za su tsara yadda za a amshi mulki domin ci gaba da gudanuwarsa yadda ya kamata.”

Ta’addanci da cin-hanci sun shiga uku

Umar Rayyan, a Abuja
Zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kwanan nan za a kawo karshen matsalar Boko Haram tare kuma da fustantar matsalar cin-hanci da rashawa a kasar nan. Ya bayyana hakan ne a jawabinsa a Abuja jim kadan bayan Hukumar Zabe ta kasa ta ba shi takardar shaidar lashe zaben Shugaban kasa.
Janar Buhari ya ce: “Shakka babu, kasar nan ta tsinci kanta a cikin mawuyacin hali a baya-bayan nan, babbansu shi ne matsalar kungiyar Boko Haram. Shakka babu lokacin yaki da ’yan ta’adda za mu fuskanci aiki mai tsauri da kuma wahala. Amma ina mai tabbatar muku cewa za mu zage damtse domin murkushe ayyukan kungiyar Boko Haram daga kasar nan. Kuma za mu dawo da zaman lafiya a yankunan da rikicin ya shafa. Ba za mu gajiya ba har sai bayan mun samu galaba bisa ’yan ta’adda, ” inji shi.
“Bugu da kari, za mu dage wajen yaki da wata matsala da ta fi ta ta’addanci muni – wato matsalar cin-hanci da karbar rashawa. Cin-hanci yana barazana ga kasar nan da cibiyoyinta da kuma kabi’un ’ya’yanta. Inda ake karkata dukiyar al’umma domin biyan bukatun wasu tsiraru. Wannan ya sa jama’a samun arziki ta hanyar da ba ta dace ba. ”
“Irin wadannan haramtattun dabi’un su ne suke zagon kasa ga mulkin dimukradiyya saboda masu yin hakan sun yi amannar cewa kudin da suka mallaka za su iya amfani da su wajen sayan gwamnati. Za mu kawo karshen wannan barazanar da take fuskantar attalin arzikinmu da ci gaban dimukradiyyarmu. Na nanata cewa cin-hanci ba abu ba ne da za mu lamunta, kuma ba za mu bari a ci gaba da daukaka shi ba a kasar nan. ”
Sabon Shugaban ya ci gaba da cewa : “Ina kiranku da mu hada hannu wajen maganin wannan matsalar da sauran kalubalen da ke fuskantarmu. Akan wadannan za mu samu nasara, amma har ila yau za mu fuskanci ’yan wasu matsaloli. Za mu yi kura-kurai. Amma ba za mu dauki lamarin da wasa ba, kuma ku kwana da sanin cewa kura-kuranmu za su bijiro ne daga rauninmu wajen tausayi da zage damtse, amma ba daga nuna halin ko-in- kula ba.

…Akwai jan aiki a gabanmu
Salihu Makera, a Abuja
Zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akwai jan aikin a gaban gwamnatinsa a kokarinta na gyara al’amuran da suka tabarbare da inganta wadanda suke tafiyar hawainiya tare da kara farfado da wadanda suke tsaye.
Janar Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi bayan ya karbi takardar shaidar samun nasarar zaben Shugaban kasa a hedkwatar Hukumar Zabe ta kasa (INEC) a shekaranjiya Laraba a Abuja.
Janar Buhari ya ce, za su fara gudanar da gwamnatinsu da rarrafe, sannan tafiya, sannan su sheka da gudu wajen gudanar da ayyukan da aka zabe su su yi, ya ce, “Na lura da abubuwan da mutane suke fata daga gare mu a yau suna da yawa, kamar yadda sadaukarwarsu ga canji ke da karfi, kuma yakininsu ke tsaye daram. Kuma a yayin da muka yi alkawarin yin bakin kokarinmu ba tare da bata lokaci ba, muna kuma rokonsu da su lura da tabarbarewar halin da muka samu kanmu a ciki, ta yadda tunaninmu zai dace da gaskiyar abubuwan da ke akwai game da abin da muke fata.”
Zababben Shugaban kasa, ya kara da cewa: “Za mu jagorance ku kamar yadda kuke bukata. Ba ku bata kuri’unku ba. Ba yanzu ’yan Najeriya suka zabenmu ba, kuma ba wannan ne lokaci na farko da ake lissafa su ba; amma wannan ne lokaci na farko da aka bari aka kirga wadannan kuri’u. Kuma da taimakon Allah, mun yi alkawarin yin duk abin da za mu iya domin farfado da Najeriya kamar yadda kuke so.”

Jam’iyyar PDP ta zama ’yar adawa a majalisa
Bashir Musa Liman, a Abuja
Bayan shekara 16 da jam’iyyar PDP ta kwashe a matsayin mai rinjiye a majalisar dattawa a yanzu ta koma ’yar adawa, bayan jam’iyyar APC ta samu kujeru fiye da 60, inda ta zama mai rinjaye a majalisar kasar nan.
A zuwa yanzu da Hukumar zabe ta INEC ta sanar sakamakon zaben sanatoci Jam’iyyar APC ta samu fiye da sanatoci 60, inda 109 shi ne yawan sanatoci da ke majalisar kasar nan.
A zaben da aka gudanar a ranar Asabar jam’iyyar PDP ta samu lashe dukkan kujerun sanatoci 15 a shiyyar Kudu maso Gabas, inda take da sanatoci 16 a cikin 18 da ke shiyyar Kudu maso Kudu. Idan har jam’iyyar PDP ta lashe zaben kujerar sanata ta Jihar Edo ta Tsakiya, inda har zuwa yanzu ba a kai ga sanar da sakamakon zaben ba, jam’iyyar za ta samu kujera 17 a cikin 18 da ke Kudu maso Kudu.
Amma duk da wannan nasarar a wadannan shiyyoyin hakan bai ba jam’iyyar PDP rinjiye a majalisar dattawa ba.
Jam’iyyar APC ta samu babbar nasara a shiyyar Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas da kuma Kudu maso Yamma.
A shiyyar Kudu maso Yamma, APC tana da kujerar sanata 13 a cikin 18, inda jam’iyyar ta rasa kujerar sanata 3 da ke Jihar Ekiti, ta kuma rasa kujera 1 a Jihar Ondo da Ogun.
A shiyyar Arewa maso Yamma, jam’iyyar PDP ta samu kujerar sanata 1 a Jihar Kaduna, inda APC take da kujera 20, wannan shiyyar ita ce shiyyar da jam’iyyar APC tafi samun rinjaye a dukkan shiyyoyin kasar nan.
A Arewa maso Gabas jam’iyyar PDP ta lashe kujerar sanata 3 da ke Jihar Taraba da kuma kujera 1 a Jihar Yobe, inda sauran kujera 13 da ke shiyyar jam’iyyar APC ta lashe su.
A shiyyar Arewa ta Tsakiya kuwa jam’iyyar PDP ta lashe dukkan kujerun sanata da ke Jihar Filato, sannan ta samu kujera 1 a Jihar Nasarawa da kuma Benuwai.
Bayan an hada jimullar kujerun ne jam’iyyar APC ta samu rinjaye a majalisar dattawa, inda ta samu kujera fiye da 60, dalilin da ya sa PDP ta zama ’yar adawa a majalisar kasar nan a karo na farko tun bayan da aka dawo mulkin farar hula a shekarar 1999.
A yanzu jam’iyyar PDP tana da sanatoci 46 kafin a fitar da sauran sakamakon zabubbuka 3.
Idan ba a manta ba PDP ta kusa rasa rinjayenta a majalisar wakilai a lokacin da ’yan majalisar suka yi yayin canza sheka daga jam’iyya zuwa jam’iyya.
A yanzu da APC ta samu rinjiye a majalisar dattawa dan majalisar da zai zama abin tausayi shi ne shugaban majalisar dattawa Dabid Mark, wanda ya shafe shekara 8 a matsayin shugaban majalisar.
A yanzu har fara hasashen babban mukamin da Dabid Mark zai iya samu shi ne mukamin shugaban marasa rinjaye, inda APC za ta samar da shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa da shugaban masu rinjaye da kuma mukamin babban mai tsawatarwa.
Sai dai duk da haka APC ba ta samu rinjayen kashi biyu bisa uku ba, wato ta samu sanatoci 73.