Kowa tasa ta fisshe shi

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta  kara dagewa bisa kokarinta  na fadada yakin da take yi da rashawa da cin hanci fiye da inda ta tsaya a halin yanzu kan binciken almundahanar da ake zargin tsoffin  shugabannin gwamnati,  ko manyan jami’anta, wadanda ake ganin shafaffu ne da mai, ba su tabuwa  ga kowa.  Wani rahoton da  Ministan […]

Kowa tasa ta fisshe shi
Kowa tasa ta fisshe shi

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta  kara dagewa bisa kokarinta  na fadada yakin da take yi da rashawa da cin hanci fiye da inda ta tsaya a halin yanzu kan binciken almundahanar da ake zargin tsoffin  shugabannin gwamnati,  ko manyan jami’anta, wadanda ake ganin shafaffu ne da mai, ba su tabuwa  ga kowa.  Wani rahoton da  Ministan Shari’a ya fitar ya umurci hukumomin bincike  na EFCC da kuma ta ICPC da su waiwayi tsofaffin batutuwa ko zargin almundahanar da aka rigaya aka yi cikakken bincike game da su kan wasu tsofaffin gwamnoni 31. Ministan kuma ya nemi  a hanzarta samar da kwafen takardun binciken da aka yi, a kuma gaggauta aikewa da su ofishinsa ba tare da bata wani lokaci ba.
Talakawa dai na goyon bayan gwamnati game da wannan yunkuri don gano wadanda suka aikata zamba da dukiyarsu  da kuma daukar matakan  hukunta su ko kuma ladabtar da su, a kuma kwato dukiyar da aka yi rub-da-ciki bisanta, suna kuma zuba  ido don ganin  lallai an kai ga biyan bukatar Ministar Shari’a ta neman a sake waiwayar wadancan tsofaffin gwamnonin da aka rigaya aka bincika da niyyar hukunta wadanda aka samu da laifi. To, amma sai dai hankulan talakawa ba su kwanta ba, saboda  fahimtar da suka yi cewa  sakamakon aikace-aikacen hukumomin bincike da manema labarai suka yi ta yayatawa,  ba su yi wani tasirin a-zo-a-gani ba har yanzu.  Babu wani abin da ya wakana ga wasu jiga-jigan kusoshin gwamnatin da ta shude, kuma kwarmato da hayaniyar da ta biyo  bayan zarge-zargen da aka yi musu sun lafa lif kamar an yi ruwa an dauke, ba wani mai waiwayarsu, domin kuwa bisa ga dukkan alamu an jefa su a mala. Hakan kuwa bai dace ba da sabon tsarin da aka yi wa kundin dokokin  kasar nan a ‘yan kwanakin nan, don bayar da dama ga kotuna su gaggauta yanke  hukunci kan batutuwan da ke gabansu.  Fatan talakawa dai shi ne kada a wannan kokarin da za a yi na yin zargaggun da tsofaffin gwamnonin da za a gano, wadanda suka sha ta fi cikinsu ya zame aikin  ‘Baban Giwa,’ ko kuma ya kasance kunshi ne a baraka, an yi ne, ba a yi ba.
Yanzu haka dai akwai zarge-zarge masu nauyi da aka yi wa wasu manyan jami’an gwamnati da na soji da ke bakin aiki, wadanda kuma ya kamata gwamnati ta bincika don ta kwantar da hankulan masu yin haka, ko domin ma ta tsira  da mutuncinta daga gani-ganin da wasu ke yi mata na kare wasu daga bincike ko hukunci. Shi ya sa talakawa suka kosa su ga yadda Ministan Shari’a da kuma hukumomin bincike  da ke karkashinsa za su tunkari  zargin da ake yi wa wasu da ake ganin tamkar ‘ya’yan  mowar gwamnati ne, wadanda ba ta so ko tsinke ya taba su. Sunayen  tsofaffin gwamnonin da ke kunshe a takardun  da aka tura wa Ministan Shari’a na daga cikin  rukunin wadancan mutanen da ake gani ba su tabuwa, domin kuwa sun san komai, idan aka  zargo su, za su yi tonon sililin da zai ba kowa mamaki. Wasu daga cikinsu ma baicin shari’ar da ake yi da su yanzu haka a gaban kotuna, sun kai ga darewa manyan mukamai a matsayin zababbu ko nadaddu, kuma muddin ba an yi cikakken bincike ne ba game da su, to fa  za a yi saken da zai sa dan zaki ya girma, dan-sane ya zame kasurgumin  macuci cikin ruwan sanyi
Kamar dai yadda rahoton bincike ya nuna akwai gagga-gaggan ‘yan siyasan da yanzu haka suka yi derere bisa manyan mukamai, musamman ma a majalisar dattijai, ciki har da shugabanta, Dokta Bukola Saraki da  wasu hamshakan gwamnoni guda 11 da ke zaune dirshan kan kujerun majalisar yanzu haka. Akwai kuma wasu  tsofaffin gwamnonin da ba su cikin majalisar dattijai a halin yanzu, amma suna can suna bushasharsu da abubuwan da suka tsira da su, suna ta cin duniyarsu anini-anini, ba su zullumin komai, ba kuma  ruwansu da kowa.
To, sa’ilin da talakawa ke bayar da cikakken goyon baya ga yakin da ake yi da rashawa da cin hanci da kuma ha’inci, don a tabbatar an bugi karfe  a lokacin da yake da zafi, sai kuma a nemi Ministan Shari’a da ya turza wajen ganin an dauki kwararan matakan kammala batutuwan da yanzu haka ke gaban alkalai, an kuma kammala su  bisa adalci da sanin-ya-kamata. Kowa na sane da yadda aka samar da wani kwamitin musamman don bayar da shawara ga shugaban kasa game da batun yaki da rashawa da cin hanci a karkashin Farfesa Itse Sagay, don samar da  ingantacciyar hanyar gurfanar da wadanda ake zargi da aikata rashawa da ha’inci a gaban kotuna, domin bayar da gudumuwar da za ta kai ga samun nasara a dambarwar da ake yi da  azzaluman da aka zarga da kokarin tsiyata kasar nan.
Ashe ke nan gudummawar da wannan kwamitin zai bayar, tare da goyon bayan talakawa zai sa a samu canjin hali  game da yadda ake gabatar da laifi gaban kotuna da kuma yadda ake binciken gano irin almundahanar da suka tattafka.  Kamar dai yadda shugaban kwamitin ya bayyana, muddin  dai wanda aka zarga zai fadi gaskiyar tabargazar da ya tafka don a yi masa sassauci yayin hukunci, to hakan zai sa kowa ya san matsayinsa, a cashe tsakanin zabiya da mai molo, ba kare bin damo.  Ka ga cikin ruwan sanyi azzalumi zai amayar da dukiyar talakawa, ya kuma tafi gidan maza ya yi ta cin gabza. Wannan shi ne ake gani abin da zai yi wa tsofaffin gwamnonin  da aka zarga kyau, idan su ma sun yi kyawun kai, su fayyace abin da suka sani don kar su wahalar da shari’a, daga baya idan aka tabbatar da zargin da ake yi musu ido ya raina fata, bayan an lafta musu shekarun da za a yi a gidan jarun, saboda samunsu da laifin ha’inci da kuma wahalar da shari’a.
To, idan a hannun hukumomin EFCC da ICPC, wadanda suka yi musu lalama yayin da suka  fara bincikensu tun can farko, suna ta wutsattsari, har ta kai aka yi musu talala mai kamar sake, yanzu za su shiga hannun da ba za a  yi musu sassauci ba, sai  dai gaskiyarsu ta fisshe su.  Yanzu dai ba sauran wani nuku-nuku, domin kuwa ana cewa ranar wanka ba a boyon cibi, haka nan kuma ranar tayar da balli ba  wata rigar kariya. Kinja Allaye in ji Babarbaren da ya sha mari, duniya fa ke nan, ana fargabar zuwan hisabi, yaya kuma  za a yi da na kiyama?  Ai  game da haka sai a ce kowa  tasa ta fisshe shi, kawai.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos