Kowa ya fara da gyara kansa

Sau da yawa akan sami Sarakunan Musulunci da Malamai da Attajirai wadanda suka kamata su hana barna, amma akan neman duniya sun bar Allah sun shiga bata, yayin da ake samun arna da kafirai suna rububin shiga musulunci saboda yadda yake a littafin Allah da hadisan Annabi (S.A.W) ingantattu. Malaman addini, attajirai da masu mulkin […]

Kowa ya fara da gyara kansa
Kowa ya fara da gyara kansa

Sau da yawa akan sami Sarakunan Musulunci da Malamai da Attajirai wadanda suka kamata su hana barna, amma akan neman duniya sun bar Allah sun shiga bata, yayin da ake samun arna da kafirai suna rububin shiga musulunci saboda yadda yake a littafin Allah da hadisan Annabi (S.A.W) ingantattu. Malaman addini, attajirai da masu mulkin siyasa da masu neman mulki, alkalai da jami’an tsaro kowa ya ga irin annobar da Annabi S.A.W ya gargadi al’umma akansu, kada mu aikata abubuwan da suke jawo su, wadanda basa jin addu’a sai dainawa: Zina, Tauye Ma’auni, Karya Alkawari, Rashin bada Zakka da rashin yin shari’a da littafin Allah mai tsarki. Duk abin da yake faruwa na daga annoba kadanne daga fushin Allah (SWT). Sai mun daina yinsu zai daina yin fushi damu, tunda ya ce ba zai canza ba sai mun canza. Duk iya addu’ar mai addu’a ba zai roki Allah ya je gona ya yi masa shuka ko noma ko girbi ba, haka Allah ba zai gina wa wani gida ko ya dinka masa riga ba. Sai dai ya roki Allah ya ba shi iko ya yi. Saboda haka addu’a tana da muhalli, mutum yana iya rokon Allah ya ba shi ilimi ko dukiya ko mulki irin na siyasa, idan Allah ya amsa sai ya samu, ko suma sai mutum ya tashi ya nema da jikinsa, ba yana kwance ba. Idan mutum bashi da wata nasaba da sarauta ko gurin matsafa yaje sai suce bai gada ba. Sai dai ya yi yaki irin na lokacin jahiliyya wanda ba’a yi yanzu. Saboda haka idan ana neman zaman lafiya da kauce wa fushin Allah kowa ya fara gyara kansa; sarakuna da masu jiran sarauta su guji yin camfi da Zina/Luwadi/Madigo.
Malaman Addini sai an tabbatar ba sa yi za a barsu su rika wa’azi da koyarwa saboda su ne suka kamata su dora al’umma akan hanya madai-daiciya ba hanyar bata ba. Malamai ne za su ilimantar da masu dukiya yadda za su fitar da zakka da wadanda Allah Ya ce a baiwa, malamai ne da alhakin dora masu mulki kan yadda za su rika gudanar da mulkin nasu cikin adalci, dama alkalai asalinsu malamai ne kamar lauyoyi da alkalai na Penal Code. Duk masu mulkin da suka saba tilas, a hukuntasu dai-dai da kowa kamar yadda ake yi a wasu kasashen. Idan masu neman mulki suka ga ana hukunta duk masu mulki da malamai da sarakuna da masu dukiya bai daya, dai-dai da kowanne talaka sai su yi hattara. Talakawan da suke jingina da dayan wadancan su tafka sabo ko ta’asa za su yi hattara. Duk masu bin kowanne addini a hukunta su da littafin da suka yi imani da shi. Idan haka ta samu maganar makauniyar biyayya, kwadayi da tsoro duk za su zama tarihi. Sai bin Allah Mahaliccin kowa da komai, da yin koyi da Annabi (S.A.W) a tsarkake, ba soki burutsu ba. Allah ya shiryemu, ya bamu iko mu gyara komai, kamar yadda Annabi (S.A.W) ya koyar, Allah ya saukar da “Alyaum akmaltu lakum diynikum, wa atmamtu alaikum ni’imatiy wa radhitu lakum Islama diyna.”
“Innaddina indallahil Islam.” Duk wani aiki da sunan ibadar Allah idan Annabi (S.A.W) bai koyar da shi ba, to ba msuulunci ba ne. Shi ne Annabin karshe wanda Allah Ya aiko da musulunci ta hannunsa, aka saukar masa da Alkur’ani mai tsarki cikin harshensa. Kamar yadda sauran Annabawan da aka saukar musu da nasu littattafan; Injila, Zabura da Attaura cikin harshensu. Allah cewa ya yi, ya ajiye arziki a saye da sayarwa! Ba a luwadi da madigo ba. Hukuncin masu yin luwadi da madigo shi ne, a hau da su kan tsauni mafi tsawo, a wurgosu taka, a biyosu da jifa da duwatsu, idan har ana yin shari’ar Musulunci. Shi yasa Shehunnan Malamai masu yin Luwadi, su da almajiransu suke jin tsoron a yi shari’ar musulunci, musamman aiwatar da haddi kan zina. Abin da ya dame mu shi ne, masu aikata wadannan miyagun laifukan su ne suke jawowa dukkan al’umma kowacce irin annoba, shi yasa tilas kowa ya dauki matakin hanawa gwargwadon iko. Kamar yadda Annabi (S.A.W) ya kallafa wa kowa; duk wanda ya ga barna yakau da ita, idan ba shi da iko, ya hana da baki, sai ya zama mai raunin imani, zai ki a zuci. Idan kana da mulki shi ne karfin; Alkalai, kotu da kurkuku da ‘yan sanda duk suna karkashin ka, malamai da sarakuna da attajirai balle talakawa duk suna karkashin mulkinka. Me zaka ce da Allah idan ba ka hukumta masu aikata miyagun laifuka, baka hana kowacce badala da barna ba??? Wajibi ne duk jihohin da suka yadda da Shari’ar Musulunci, gwamnoninsu su kira duk shaihunnan malamai da limaman Juma’a da masu yin tafsir da duk wadanda aka yarda su rika yin wa’azi na jihohin nasu, kowanne ya rubuta yasa hannu akan ya yarda majalisa tayi doka ta aiwatar da Shari’ar Musulunci akan kowa da kowa, kamar yadda Allah ya saukar cikin littafinsa mai tsarki. Duk gwamnan da bai yi haka ba kowa yasan munafiki ne, mayaudari, azzalumi. Haka suma ‘yan majalisun idan ba su tsara dokar ba. Wutar munafukai tana karkashin ta Yahudawa da Nasara.

Alhaji Abdulkarim daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta kasa
08060116666, 08023106666, 08173106666

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno