‘Kowa ya rike sana’arsa da gaskiya zai ga alheri’
Wani wanzami mai suna Sulaimanu Haruna, mai shekara 45 a Benin ta Jihar Edo ya bayyana sana’ar wanzanci da aiki mai muhimmanci, musamman saboda rufin asarin da ke cikinsa, sannan duk wanda ya rike sana’arsa da gaskiya, to zai ga alheri.Malam Sulaimanu ya yi wannan furucin ne a yayin wata zantawa da Aminiya a wajen […]
Wani wanzami mai suna Sulaimanu Haruna, mai shekara 45 a Benin ta Jihar Edo ya bayyana sana’ar wanzanci da aiki mai muhimmanci, musamman saboda rufin asarin da ke cikinsa, sannan duk wanda ya rike sana’arsa da gaskiya, to zai ga alheri.
Malam Sulaimanu ya yi wannan furucin ne a yayin wata zantawa da Aminiya a wajen sana’arsa, inda ya kara da cewa akwai taimaka wa al’ummar duniya. “Wannan taimako kuwa ya hada da duk wadansu al’amura da suka shafi lafiya a sassan jiki daban-daban. Muna da kayan aikin da suka hada da asake da reza na aski da na cire ’yar wuya da na kaciya da na bangaren yin kaho da balli-balli da saifa da sauransu. Gudanar da irin wannan aiki dole sai an lakance shi”. Inji shi.
Malam Sulaimanu ya ce, “Wanzanci gadon gidanmu ne, domin tun ina yaro na koye shi a wurin mahaifina. Ba ni da wata sana’ar da ta wuce wanzanci. A cikinta na yi auren fari da na biyu kuma Allah Ya ba ni ’ya’ya maza da mata. Alhamdulillahi, ina cikin rufin asiri, saboda haka ne ma nake kira ga ’yan uwana wanzamai da su kasance masu yin gaskiya cikin wannan sana’a, domin a samu gamawa da duniya lafiya, cikin rufin asiri”.