Kowa zai samu katin zabe na dindindin – Jega

Shugaban Hukumar Zabe ta kasa Farfesa Attahiru Jega ya tabbatar wa ’yan Najeriya duk wanda ya yi rajista zai samu katin zabensa kafin nan da 14 ga Fabrariru mai zuwa. Farfesa Attahiru Jega ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba, lokacin da yake bayani wa manema labarai a fadar Shugaban kasa jim kadan da fitowarsa […]

Kowa zai samu katin zabe na dindindin – Jega
Kowa zai samu katin zabe na dindindin – Jega

Shugaban Hukumar Zabe ta kasa Farfesa Attahiru Jega ya tabbatar wa ’yan Najeriya duk wanda ya yi rajista zai samu katin zabensa kafin nan da 14 ga Fabrariru mai zuwa.

Farfesa Attahiru Jega ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba, lokacin da yake bayani wa manema labarai a fadar Shugaban kasa jim kadan da fitowarsa daga wurin da aka rantsar da sabon Kwamishinan Zabe Farfesa Akinola Murtala Salawu.
“Duk dan Najeriyar da ya yi rajista zai samu rajistarsa kafin ranar 14 ga Fabrairu da yardarm Allah,” inji Jega.
A lokacin rantsuwar Shugaba Goodluck Jonathan ya bukaci Hukumar INEC ta zama ’yar ba ruwanmu a yayin gudanar da zaben mai zuwa domin ta samu damar gudanar da zabe mai inganci.
Shugaba Jonathan ya ce ’yan Najeriya sun damu kan ko INEC za ta iya gudanar da ingantaccen zabe a bana. “Akwai bukatar INEC ta zama ’yar ba ruwanmu yayin gudanar da aikinta don ta yi zabe mai inganci saboda haka duniya ta zuwa wa INEC ido, kuma kai (Salawu) ka zo ne a lokaci mai wahala ana saura kwana 40 a yi zabe. Don haka ka zo a lokaci mai wahala, kuma ina da yakinin shugaban hukumar wanda yake nan yana bukatar aikinka.”
Shugaba Jonathan ya ce Farfesa Jega zai so a ce ya ninka yawan ma’aikatansa inda yana da kudi, don sauke wannan nauyi saboda ’yan Najeriya suna nuna damuwa a kan ko INEC za ta iya gudanar da zaben.”
Daga nan sai Shugaba Jonathan ya umarci Farfesa Attahiru Jega ya tabbatar dukan ’yan Najeriya sun samu katin jefa kuri’a na dindindin.
Ya ce, bai kamata a gudanar da zabe mai zuwa idan dai za a hana wadansu ’yan Najeriya ’yancinsu na jefa kuri’a.
Jonathan ya nanata cewa ’yan Najeriya ne za su yanke shawara kan wanda zai mulke su a zabe mai zuwa.
Ya ce wajibi ne INEC ta yi duk abin da za ta iya don tabbatar da cewa dukkan ’yan Najeriya sun samu katin jefa kuri’arsu don ba su damar kada kuri’a a lokacin zaben.
Ya ce yana sane cewa wasu gwamnoni suna kukan cewa har yanzu ba su samu katin zabensu na dindindin ba, inda ya ce hakan yana nuna ’yan Najeriya da dama ma har yanzu bas u samu nasu ba, lamarin da ya ce, ya sanya jama’a da dama cikin damuwa.

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista