Kowa zai samu ’yanci a Jihar Filato – Simon Lalong

Gwamnan Jihar Filato mai jiran gado Barista Simon Lalong ya ce a gwamnatinsa kowa zai samu ’yanci a jihar kuma gwamnatinsa ba za ta cuci kowa ba a jihar.  Zababben Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen walimar murnar cinzabensa da Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa […]

Kowa zai samu ’yanci a Jihar Filato – Simon Lalong
Kowa zai samu ’yanci a Jihar Filato – Simon Lalong

Gwamnan Jihar Filato mai jiran gado Barista Simon Lalong ya ce a gwamnatinsa kowa zai samu ’yanci a jihar kuma gwamnatinsa ba za ta cuci kowa ba a jihar. 

Zababben Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen walimar murnar cin
zabensa da Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya shirya masa a garin Jos.
Ya ce Allah Ya kawo canji a Jihar Filato, don haka in Allah Ya yarda irin miyagun abubuwan da suka faru a jihar a baya, ba za su sake faruwa ba.
Zababben Gwamnan ya yi bayanin cewa tunda farko a lokacin da muka zo wajen Malam, ya yi mana addu’a kuma ya ba mu tabbacin cewa za mu ci wannan zabe, amma babbar matsalar ita ce kare zaben. Ya ce “Nan take na yi wa Malam alkawarin za mu kare wannan zabe. Kuma a lokacin zaben na jefa kuri’a ne a Shendam ban yi barci ba, na dawo garin Jos don kare wannan zabe. Bayan da na dawo gari ya kusa wayewa, sai na samu labarin cewa wai an tafi hutu daga karbar sakamakon zaben da ake yi, saboda sakamakon zaben Jos da Wase ba su iso ba,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Nan take na ce ba a isa ba, na fara waya ko’ina, domin ba za mu dawo wurin Malam mu ce ba mu kare zaben ba. Ganin yadda baki dayan al’ummar Filato suka ce za su tafi hukumar zaben sai nan take suka janye wannan hutu suka karbi sakamakon zaben Jos da Wase muka samu nasara.”
Barista Lalong ya ce magudin zaben kujerar Sanatan Filato ta Arewa da aka yi, ba za su yafe ba, sai kotu ta yanke hukunci. Ya ce, “Sun ce mu yafe zaben Sanata su kuma za su yafe zaben Gwamna, na ce bas u ci zaben Gwamna ba, ba su ci zaben Sanata ba, don haka ba za mu yafe zaben sanatarmu ba.”
Ya ce irin makudan kudin da PDP ta kashe a lokacin yakin zabe a jihar, sun isa a biya bashin albashin ma’aikatan jihar da gina makarantu da asibitoci. Sai ya yi kira ga al’ummar jihar su ci gaba da yi musu addu’o’i tare da ba su goyon baya da hadin kai don cimma nasara.
Tunda farko a jawabin Sheikh Sani Yahya Jingir ya cewa Allah ne Ya ba Simon Lalong Gwamnan Jihar Filato. “Allah Ya yi maka gata wajen samun wannan nasara, ban sanka ba na sa aka zabe ka, amma ina yi maka kyakyawan zato domin ka samu shaida daga jama’ar jihar nan. Don haka kada ka toshe mana kofa, ka rika sauraren koke-koke jama’ar Filato,” inji shi.
Sai ya yi kira ga al’ummar Najeriya su ba sabuwar gwamnati goyon baya da hadin kai kuma su ba ta lokaci don magance matsalolin da ake fuskanta a kasar nan.