Duk alhajin Najeriya ya samu tallafin N1.6m —NAHCON
Alhazan da suka biyan kudin kujerar Hajji ta tsarin adashin gata sun fi amfana
Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta duk alhazan jihohin Najeriya da sunan sauke farali a 2024 sun samu tallafi na Naira miliyan 1.36.
Shugaban hukumar, Jalal Arabi, ya ce Gwamnatin Tarayya ta ba wa alhazan tallafin ne a sakamakon tashin Dala da faduwar darajar Naira.
Jalal Arabi ya bayyana cewa tashin Dala ya sa kudin kujerar da maniyyata suka biya, Naira miliyan 4.9 gazawa, ana bukatar kowanne ya cika miliyan N3.6.
A sakamakon hukumar ta tuntubi gwamnati domin yi wa kowane maniyyaci rangwamen farashin Dala a kan Naira 850.
- An kama lakcarorin bogi a Jami’ar BUK
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sabon Mafi Karancin Albashi Zai Iya Daidaita Al’amura
Ya ce amma a maimakon haka, gwamnati ta ba wa NAHCON Naira biliyan 90 domin cika wa kowanensu saboda gibin da aka samu a sakamakon faduwar darajar Naira.
“Mun sha wahala kan yadda za a raba biliyan 90 din ta yadda zai isa a cika wa kowane maniyyaci Naira miliyan 3.6 a kan miliyan 4.9 da suka riga suka biya.
“Sai NAHCON ta shigo da duk masu ruwa tsaki ta yadda kowanne bangare zai amfana da tallafin.
“Kowane maniyyaci ya samu Naira miliyan 1.6 daga cikin tallafin biliyan 90 da gwamnati ta bayar.
“Amma wadanda suka biya ta tsarin adashin gata sun fi amfana” in ji shugaban na NAHCON.
Jalal Arabi ya kara da cewa Najeriya ta rasa alhazai kimanin 30 a Hajjin 2024, wadanda kimanin hudu daga cikin su tsananin zafi ne ya yi ajalinsu.
Hakazalika ya bukaci masu korafe-korafe kan Hajjin 2024 da su gabatar su domin daukar matakin da ya ce.
Ya ce hukumar na maraba da duk mai wata shawara kan yadda za a inganta tsarin gudanar da aikin Hajjin 2025.