Kowane dan Najeriya na da ’yancin zama a ko’ina a kasar nan – Gbong Gwom Jos
Mai martaba Gbong Gwom Jos, Da Gyang Jacob Buba ya ce dokokin kasa sun ba kowane dan Najeriya ’yancin ya je ko’ina ya zauna a kasar nan ba tare da tsagwama ba. Gbong Gwom na Jos ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga ’ya’yan kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Jihar Filato da […]
Mai martaba Gbong Gwom Jos, Da Gyang Jacob Buba ya ce dokokin kasa sun ba kowane dan Najeriya ’yancin ya je ko’ina ya zauna a kasar nan ba tare da tsagwama ba. Gbong Gwom na Jos ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga ’ya’yan kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Jihar Filato da suka kai masa ziyarar ban girma a fadarsa da ke garin Jos.
Ya ce a doka ta ba dan kasa ’yancin ya je ko’ina ya zauna a Najeriya, abin da kawai ake bukata shi ne ya bi dokar kasa a duk inda yake a zaune. “Don haka babu wanda zai ce wani ya bar Jos, amma ya zama wajibi al’umma su yi biyayya ga duk wanda Allah Ya baiwa shugabanci a kasa,” inji shi.
Gbong Gwom na Jos ya ce akwai mutanen Jihar Filato da dama suna zaune a wurare daban-daban na Jihar Katsina amma ba su taba zuwa sun ce ana musguna musu ba. Ya ce, “Mu kanmu mun zauna a wurare daban-daban lafiya muna da abokan arziki a Jihar Katsina da kasar nan baki daya. Babu wanda ya samu riba a rikice-rikicen da aka yi a garin Jos a shekarun baya, sai dai dimbin asarar rayukan jama’a da dukiyoyin da muka yi.”
Gbng Gwom din ya ce, “Ya kamata mu dawo cikin hankalinmu mu saki jiki da junanmu mu zauna lafiya, kowa ya ci gaba da gudanar da harkokinsa ba tare da fargaba ba.”
Ya nuna farin cikinsa da ziyarar da kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna jihar suka kai masa.
Tun da farko a nasa jawabin shugaban kungiyar Alhaji Rabi’u Yahaya Bindawa ya ce sun kai ziyarar ce don girmamawa tare da kulla zumunci a tsakaninsu da fadar Gbong Gwom din.
Ya ce suna neman alfarmar fadar don su zama ’ya’ya a cikinta, domin duk abin da ya taso a neme su, kuma za su yi biyayya ga fadar kan duk abin da ya taso don bada gudunmawarsu.