Kowane gauta ja ne
Ashe dai ganin kitse ne ake yi wa rogo, sai da aka gatsa, sa’anan aka fahimci cewa ba kitsen ne ba. Jama’a da yawa sun dauka Malam Muhammadu Buhari wani hamshakin mai kudi ne, amma sai ga shi nan sa’ilin da ya bayyana wa duniya abin da ya mallaka daidai da yadda tsarin mulki ya […]
Ashe dai ganin kitse ne ake yi wa rogo, sai da aka gatsa, sa’anan aka fahimci cewa ba kitsen ne ba. Jama’a da yawa sun dauka Malam Muhammadu Buhari wani hamshakin mai kudi ne, amma sai ga shi nan sa’ilin da ya bayyana wa duniya abin da ya mallaka daidai da yadda tsarin mulki ya bukata, an gano cewa duka-duka abin da ya mallaka bai taka kara ya karya ba, a matsayinsa na mutumin da babu hurumin mulkin kasar nan da bai taka rawa ba.
Wannan ne ya sa ake ta mamakin yadda har yanzu tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da wasu gwamnonin da suka sauka da kuma manyan jami’an gwamnatinsa ba su bayyana abin da suka mallaka ba bayan saukarsu. Ba ma wadanda suka rigaya suka hau, suka kuma sauka ba, hatta wasu gwamnonin da ke bisa karaga ba su yi haka ba, kuma sai ga shi nan suna ta hayaniya da hayagaga cewa an tsiyata gwamnatin da suka gada, ba a bar musu ko ranyau ba a cikin baitul-mali, kuma hakan ya hana su biyan albashin ma’aikata, balle gudanar da wasu ayyukan alheri.
Yanzu haka akwai gwamnoni kusan 21 da ba su iya tabuka katabus, hatta kwamishinoni ma sun kasa nadawa saboda rashin kudi, domin tsofaffin gwamnonin da suka sauka sun farke dukiyar da suka karkashe yayin yakin neman zaben da suka yi shekara hudu da suka wuce. To idan kuwa haka ne me zai hana gwamnoni masu ci a halin yanzu turzawa don neman kudin da za su fara gudanar da harkokin mulki, ba tare da jiran Gwamnatin Muhammadu Buhari ta rika sanya musu loma a baka ba.
Ai tun da farko kamata ya yi a ce duk dan takarar mukamin Gwamna wajibi ne ya san irin halin da tattalin arzikin jiharsa ke ciki kafin ya fara neman darewa kujerar mulki, domin kuwa ba sabon abu ba ne a ce wani sabon Gwamna bai gaji ko tasa ba daga Gwamnan da ya bar gado. Wadanan abubuwa ne da aka kasa magancewa, aka kuma bari suka zama hujjoji ga sababbin gwamnoni wajen kasa gudanar da ayyukan da ke gabansu, daga bisani kuma su mike kafa, su shiga shirga satar dukiyar jama’a ba kakkautawa, kamar yadda magabatansu suka yi domin abin ya zama tamkar gado, ko kuma gasa.
Babban abin takaici, ko abin haushi ko abin dariya game da irin wannan harkar, shi ne, sai ka ga gwamnonin da suka jahilci ainihin halin tattalin arzikin da jiharsu ke ciki sun fi kowa hankoron yin alkawura marasa kan gado, wadanda ba su da tushe balle wata makama don darewa kujerar mulki. Sa’anan kuma da zarar sun hau mulki babu wani Gwamna da ke tuntubar jama’a don neman shawarwarinsu game da ayyukan kirki da ya kamata ya yi, sai dai ka ga kawai yana bin son ransa da biye wa zuciyarsa wajen aiwatar da dukkan ayyukan da ya ga dama gaba-gadi.
Da zarar an zabi Gwamna to, zai mance da batun rashin kudi a baitul-malinsa, ya komo ba ruwansa da jama’arsa, sai kansa kawai ya sani, shi ne gaba da kowa, tilas ne kowa ya koma bayansa, ya kaskantar da kansa, ko kuma ya gamu da gamonsa. Shi ke nan, daga nan Gwamna zai buwayi kowa, ba mai ja da shi, domin ya zama dodon da kowa ke tsoro, yana kuma yi masa bauta. Shi kuma sai ya dauki wani girman kai da fadin rai ya dora wa kansa, ya rika jin cewa ya rika, har yana iya kashewa da rayawa. In da duk ya je, sai ka ji yana wa kansa kirari, yana cewa “ina wani ba ni ba?” Babu abin da zai mayar da hankalinsa a kai kamar batun dukiya da kuma yadda zai tara ta.
Ta haka nan sai ya zame dagutu ga sauran ‘yan siyasa ‘yan uwansa, kuma gidansa ya komo tamkar ‘Madinatul-Munawwara,’ saboda yawan ziyara, fuskarsa kuma ta zama alkibla, ita za a yi ta kalla, ‘yan baranda kuma su zagaye shi, suna ta tumasanci. Wanda duk ke neman wani mukamin siyasa sai ya kama kafarsa, mai neman ya gaje shi sai ya mayar da kansa wawa kafin a amince masa ya kai ga biyan bukatarsa. Tilas ne kuma mabiyansa su gwanance wajen kwatanta halayensa na yin amfani da rashawa don ganin alfanun dukkan al’amuran da aka sanya a gaba.
Al’amarin rashawa na da wuyar sha’ani, domin yakan cutar da kowa, da mai karba har ma da mai bayarwa. Ai ya kamata sababbin gwamnonin da ke korafin cewa an tsiyata jiharsu kafin hawansu karagar mulki su fahimci cewa ai kudin talakawa ne aka wawushe don a toshe bakunan talakawa, a kuma share musu fagen hayewa kujerar Gwamna. Shi ya sa wasunsu suka kasa yin komai don kwato dukiyar talakawar da magabatansu suka barnatar, sanin cewa haka nan za su yi, domin kowane gauta ja ne.
Babu dai wanda sababbin gwamnonin nan za su ruda da hawayen kukansu, game da rashin kudin batarwa a hannunsu, domin talakawa sun gane cewa wayonsu na korar kare daga gindin dinya ne don a ci. An dai ga yadda sababbin gwamnoni suka hau mulki a yankwane, kamar iska za ta hure su, amma kafin kwana 100 bisa mulki sai suka murje, fatarsu ta cika, tana sheki shar, sun yi kiba bul-bul, kumatunsu sun ciccika, sa’anan sun ajiye ‘yar kwajajar teba. To tun da an samu rana, an kuma shanya gauta, sai mu jira, mu ga yadda zai zama ja-wur.