Koyar da likitanci da Hausa zai inganta ilimi a Najeriya – Maidoki
SadaukinSakkwato Injiniya Muhammad Lawal Maidoki, ya ce yana goyon bayan maganar da Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yi cewa a fara koyar da ilimin likitanci da na injiniya da harshen Hausa, domin hakan zai kara inganta ilimi a Najeriya. Injiniya Lawal Maidoki ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da […]
Injiniya Muhammad Lawal Maidoki
SadaukinSakkwato Injiniya Muhammad Lawal Maidoki, ya ce yana goyon bayan maganar da Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yi cewa a fara koyar da ilimin likitanci da na injiniya da harshen Hausa, domin hakan zai kara inganta ilimi a Najeriya.
Injiniya Lawal Maidoki ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a Gombe, inda ya ce kishin kasa shi zai sa a goyi bayan wannan tsari na koyar da ilimin boko da harshen Hausa.
Ya ce amfani da harshen wadansu shi ne silar koma bayan kasar nan wajen tabarbarewar ilimi saboda harshen Ingilishi ba harshenmu ba ne. Ya ce koyar da kowanne sashi na kimiyya da Hausa zai taimaka duk da cewa akwai harsunan Ibo da Yarbanci, idan ba su gamsu ba a koyar musu da harshensu hakan zai taimaka.
Ya ba da misali da kasar Thailand da Najeriya ke dogara da shinkafarta, inda ya ce da harshen kasarsu suke karatu ba da Ingilishi ba, “Don me ya sa mu ba za mu yi kishin tamu kasar da harshen Hausa ba?”
Ya kara da cewa kasashen Japan da Malesiya da harshensu suke karatu, kuma yawan mutanen kasar Malesiya ba su kai yawan mutanen da ke Arewacin Najeriya ba.
A cewarsa, yanzu idan dan wata kasa ya je kasar Bulgeriya zai yi karatu sai ya yi zaman koyon harshen kasar na shekara biyu kafin ya fara karatu. “Ashe kishin harshenka shi ya fi kamata da kai,” inji shi.
Ya ce muddin ci gaban Najeriya ake so, dole a dawo amfani da harshen Hausa. Ya ce kuma hatta majalisun dokoki na jihohin kasar nan yana da kyau su koma yin Hausa ba Ingilishi a lokutan zaman majalisun.
Malam Lawal Maidoki ya ce “Nasarar hakan ba zai samu ba sai ’yan jarida sun ba da gudumawarsu wajen yayata wannan batu.”
Ya ce hatta ilimin kere-kere idan ana koyar da shi da harshen Hausa, za a fi fahimta kuma Najeriya za ta ci gaba.