‘Koyar da tarihin sahabban Annabi maganin halaka ne’

Baban Limamin Masallacin Juma’a na Deidei da ke yankin Birnin Tarayya, Abuja, Sheikh Abubakar Ibn Abubakar ya yi kira ga malaman addinin Musulunci su rika bai wa dalibansu ilimin tarihin sahabban Annabi Muhammadu (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi), domin guje wa halaka.Sheikh Abubakar ya yi kiran ne lokacin da yake gabatar […]

‘Koyar da tarihin sahabban Annabi maganin halaka ne’
‘Koyar da tarihin sahabban Annabi maganin halaka ne’

Baban Limamin Masallacin Juma’a na Deidei da ke yankin Birnin Tarayya, Abuja, Sheikh Abubakar Ibn Abubakar ya yi kira ga malaman addinin Musulunci su rika bai wa dalibansu ilimin tarihin sahabban Annabi Muhammadu (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi), domin guje wa halaka.
Sheikh Abubakar ya yi kiran ne lokacin da yake gabatar da Huduba a masallacin a ranar Juma’ar da ta gabata.
Sheikh Abubakar, ya kara da cewa, rashin sanin gudunmawar da sahaban suka ba da ga yada addinin Musulunci ne shi ya sa wadansu matasa suke shiga kungiyoyin da suke suka da zagin sahabban.
Ya kara da cewa, al’adar Musulmi nagari ita ce girmama sahabbann Manzon Allah (SAW) da kuma yi musu addu’ar neman tsira da gafara a wajen Allah a yayin da aka ambaci sunansu amma ba a rika zaginsu ba.
Malamin ya ja hankalin matasa su nemi ilimin addini a wurin malaman da suke riko da Alkur’ani da kuma Sunnar Annabi (SAW).