Koyon hada abincin jarirai ya kori Tamowa daga yankinmu

Kungiyar Sasakawa ce ta musu dabarun hada abincin jarirai mai gina jiki daga abubuwan da suke nomawa

Koyon hada abincin jarirai ya kori Tamowa daga yankinmu

Wata uwa a garin Filiya na Karamar Hukumar Shongom a Jihar Gombe ta ce koyon hada abincin jarirai mai gina jiki daga abubuwan da suke nomawa ya fatattaki cutar Tamowa daga kauyukansu.

Ladi Naftali ta ce kungiyar Sasakawa ce ta koya musu hada abincin jarirai mai gina jiki, irin su kunun gero da ake hadawa da waken suya da gyada a markada ana ba yara, baya ga shayar da yara ruwan nono.

Ladidi ta ce bayan ta koyi hada abincin jarirai mai gina jikin, ta koyar da matan karkararsu da matan Fulani makiyaya da ke yankin kuma sun ce suna ganin alfanun hakan.

A cewarta, wannan tsari da suka bi ya kawar da cutar Tamowa a tsakanin ’ya’yansu da kusan kashi 85 cikin 100 a karkararsu.

Ta bayyana cewa Sasakawa ta kuma koyar da su dabarun shayar da jarirai nonon uwa zalla da dabarun rike nono ta yadda yaro zai sha ya koshi, da yadda za su tsayar da shi ya huta, sannnan su sake ba shi dayan ma ya sha.

Ta ce bayan yaro ya yi wata shida yana shan nonon uwa zalla, sai su fara hada masa abincin yara da zai kara gina masa jiki.

Ladidi yaba wa Sasakawa bisa horon da ta musu na dabarun noma da sarrafa abinci da kuma hanyoyin samun kudin shiga a kananan sana’oi.

A cewarta, kafin zuwan Sasakawa ba su san wannan tsari ba, amma yanzu an koya musu sun kuma ga canji.

Sannan ta yi kira ga mata da su yi koyi da tsari dan zai kara taimaka musu wajen rage kashe kudin zuwa asibiti neman magani kan jinyar cutar Tamowar ’ya’yansu.

Daga nan sai ta yi fatan shirin zai dore a Najeriya domin su koyi wasu dabarun tunda yanzu bayan samun saukin rayuwa harda karin samun hanyoyin shigar kudi.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos