Ku ba ni canji

Wani Bafulatani ne da Babarbare suka shiga motar haya a tasha za su je wani gari. Suna cikin tafiya sai barayi suka tare su, suka amshe kudin kowa. An zo wajen Bafulatani sai ya ce ba shi da ko kwabo. Shi kuwa Babarbare sai aka same shi da bandir-bandir din kudi sababbi ’yan Naira ashirin-ashirin, […]

Ku ba ni canji
Ku ba ni canji

Wani Bafulatani ne da Babarbare suka shiga motar haya a tasha za su je wani gari. Suna cikin tafiya sai barayi suka tare su, suka amshe kudin kowa. An zo wajen Bafulatani sai ya ce ba shi da ko kwabo. Shi kuwa Babarbare sai aka same shi da bandir-bandir din kudi sababbi ’yan Naira ashirin-ashirin, barayi suka amshe. Har an ce kowa ya shiga mota su tafi, sai Bafulatani ya ce wa barayi: “Don Allah cikin sababbin kudin nan ku ba ni canji.”

Daga Ibrahim Hassan Gobir, 09034088846