Ku bar jama’a su fadi ra’ayinsu kan taron kasa – Fashola
Gwamnan Jihar Legas Mista Babatunde Raji Fashola ya shawarci kwamitin duba yiwuwar taron kasa su saurari bayanan da jama’a za su yi musu kuma su ba kowa damar fadin albarkacin bakinsa koda abin da zai fada ba zai yi musu dadi ba. Gwamna Fashola yana magana ne lokacin da yake karbar bakuncin kwamitin a ofishinsa, […]
Gwamnan Jihar Legas Mista Babatunde Raji Fashola ya shawarci kwamitin duba yiwuwar taron kasa su saurari bayanan da jama’a za su yi musu kuma su ba kowa damar fadin albarkacin bakinsa koda abin da zai fada ba zai yi musu dadi ba.
Gwamna Fashola yana magana ne lokacin da yake karbar bakuncin kwamitin a ofishinsa, inda ya ce idan ba haka aka yi ba za a bar wani bangaren al’umma yana guna-guni, kuma haka ba zai sa a cimma burin taron ba.
Gwamnan ya ce akwai bukatar a sake duba taron sake fasalin siyasa da aka yi a shekarar 2006, domin duba wasu batutuwa a cikinsa da za su amfani kasa. “Ba shakka za a samu wasu batutuwa masu ma’ana a wancan tattaunawa da aka yi, kuma yin hakan ba zai zamo bata lokaci da kudi da basira ba da aka yi domin wancan aiki na 2006.
Fashola ya ce in za a tattauna, to tilas ne a ce ga abin da ake son a tattauna a kai domin jama’a su san ina aka dumfara kuma ina za su ba da gudunmawarsu.
Ya ce wannan shi ne karo na farko da ya rubuta jawabi lokacin da zai karbi baki a shekara 6 da suka gabata, ya ce ya yi haka ne saboda muhimmacin da yake kallon wannan yunkuri na taron da kuma wasu batutuwa masu cin rai kamar abin da ya faru a Jihar Edo lokacin da kwamitin ya kai ziyara can.
Gwamnan ya ce da yawa ’yan Najeriya ba su da kwarin gwiwa kan zabbbun wakilai na su yi musu wannan aikin, don haka ya ce idan an ce za a tattauna to tilas ne a samu ra’ayoyi mabambanta daga bisani a yi matsaya a kansu.
Shugaban Kwamitin Dokta Femi Okorunmu ya yi wa Gwamnan godiya kan irin tarbar da ya yi musu da kuma shawarwarin da ya ba kwamitin.