Ku daina tsine wa shugabanni, ku bar su da Allah — Sarkin Musulmi

Sarkin ya gargaɗi shugabanni da su ji tsoron haɗuwarsu da Allah.

Ku daina tsine wa shugabanni, ku bar su da Allah — Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Sa’ad Mohammad Abubakar II, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su daina la’antar shugabanninsu, face su bar su da Allah Ya hukunta su.

Ya jaddada cewa babu abin da yake dawwama a duniya – ko da na gari ne ko akasin haka.

Sarkin ya buƙaci ‘yan Najeriya su ci gaba da yi wa ƙasa da shugabanninsu addu’a, tare da jan hankali kan muhimmancin haɗin kai da dogaro ga Allah wajen shawo kan matsalolin ƙasar nan.

Da yake jawabi a wajen taron sauyin yanayi da tashe-tashen hankula a Arewacin Najeriya, Sarkin ya tunatar da shugabanni cewa za su amsa tambayoyi a gaban Allah Maɗaukakin Sarki.

“A ranar nan, kowa zai tsaya shi kaɗai, babu wanda zai kawo masa agaji. Babu mataimakin gwamna ko mai bayar da shawara da zai tsaya maka.

“Mu ji tsoron Allah a duk abin da muke yi, kuma mu yi wa ƙasarmu addu’a,” in ji shi.

Ya kuma gargaɗi malaman addini kan dulmiyar da mabiyansu don amfanin kansu, inda ya jaddada cewa yawancin mutane na gaskata malamai da abin da suka faɗa.

Sarkin, ya yi tsokaci kan tasirin rabuwar kai a tsakanin al’umma, inda ya ce masu son ganin Arewa ta samu koma baya ne ke yawan kawo rashin fahimta.

“Idan muka haɗa kai, za mu iya shawo kan kowace irin matsala. Yawan kalaman ɓatanci da ake yi ana yi ne domin kawo rabuwar kai,” in ji shi.

Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), Rabars Dokta D.C. Okoh, ya amince da batun sauyin yanayi a yankin, da kuma illolin da yake haifarwa ga al’umma.

Ya yi kira da a ɗauki matakai don magance talauci, rashin adalci, da kuma samar da damar samun albarkatu don kauce wa rikici.

Rabarsn Okoh, ya kuma goyi bayan Sarkin wajen yin kira ga shugabanni da su kasance masu gaskiya da adalci.

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɓullo da wata doka wadda za ta magance matsalar sauyin yanayi don samar da makoma mai kyau.

Ya ce, “Dokar tana ƙunshe da manufofi da dabarun aiki a fannonin makamashi, kula da ruwa, da kuma noma.”

Gwamnan ya yaba da aikin da hukumar da ta shirya taron, ta yi wajen jaddada muhimmancin muhalli.

NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da CNG

Sanata Barau ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano

Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu