Ku dawo da kudin sata ko ku fuskanci hukunci – Magu
Shugaban riko na hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta Najeriya EFCC Ibrahim Magu, ya gargadi barayin gwamnatin kasar wadanda suka sace kudade da kadarorin gwamnati da su dawo dasu ko su fuskanci hukunci. Magu ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai (NAN) a New York a Amurka, inda ya […]

Shugaban riko na hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta Najeriya EFCC Ibrahim Magu, ya gargadi barayin gwamnatin kasar wadanda suka sace kudade da kadarorin gwamnati da su dawo dasu ko su fuskanci hukunci.
Magu ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai (NAN) a New York a Amurka, inda ya kwatanta rashawa a matsayin babban zunubi da hukumar ba zata ta taba yadda da ita ba.
Magu ya bukaci duk wadanda suka sace kudade da kadarorin gwamnati da su dawo dasu, sannan su shiga cikin shirin yaki da rashawa saboda muhimmancin ta.
‘Duk ‘yan Najeriya na da irin rawar da zasu taka wajen yaki da rashawa da mai laifi da mara laifin’.