Ku guji shan giya muddin ku ka kai shekara 50 – Masana

Ta shawarci wadanda suka kai wadannan shekarun da su fi mayar da hankulansu sha ’ya’yan itatuwa da sauran nau’ukan abinci mara nauyi.

Ku guji shan giya muddin ku ka kai shekara 50 – Masana

Wani mashayin giya

Shugabar Cibiyar Bincike Kan Harkar Lafiyar Abinci ta Kasa reshen jihar Ekiti, Misis Doyin Ajayi ya shawarci wadanda suka haura shekaru 50 a duniya da su guji ta’ammali da giya don kiyaye kamuwa da cututtuka.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ta bayyana hakan ne a Ado Ekiti, babban birnin jihar ta Ekiti a ranar Lahadi yayin da take zantawa da ’yan jarida.

Ta shawarci wadanda suka kai wadannan shekarun da su fi mayar da hankulansu sha ’ya’yan itatuwa da sauran nau’ukan abinci mara nauyi.

A cewarta, shan giya a wadannan shekarun zai iya yin mummunar illa ga wasu sassa na jiki kuma ya haifar da saurin tsufa.

Misis Doyin ta kuma lura cewa masu shan giyar a kai a kai na iya lalata kodarsu, inda ta ce ko da shan giyar sama-sama shima ba shi da wata fa’ida.

Daga nan sai ta yi gargadi a kan cin nau’ukan abinci barkatai, tana mai shawartar jama’a da su rika tuntubar masana domin sanin irin abincin day a fi dacewa da su.