‘Ku Ilmantar Da Mata Muhimmancin zaben ’Yan Takara Nagari’

Majalisar Kungiyoyin Mata ta Najeriya (NCWS) ta ce wayar da kan mata kan zaben ’yan takarar da suka cancanta a zaben 2023 na da matukar muhimmaci. Shugabar kungiyar, Priscila Kuye, ta bayyana wa taron shekara da suka shirya kan muhimmacin sanya mata a sha’anin gwamnati a ranar Alhamis cewa yin hakan ya zamo dole, saboda […]

‘Ku Ilmantar Da Mata Muhimmancin zaben ’Yan Takara Nagari’

Majalisar Kungiyoyin Mata ta Najeriya (NCWS) ta ce wayar da kan mata kan zaben ’yan takarar da suka cancanta a zaben 2023 na da matukar muhimmaci.

Shugabar kungiyar, Priscila Kuye, ta bayyana wa taron shekara da suka shirya kan muhimmacin sanya mata a sha’anin gwamnati a ranar Alhamis cewa yin hakan ya zamo dole, saboda yawan matan da ke fita yin zabe a Najeriya ya fi na maza.

“Kada ku bar wa maza komai, domin idan ana batun sha’anin mata ba su san inda ke mana kaikayi ba.

“Ku karfafa wa kanku da ’ya’yanku mata guiwar shiga harkokin siyasa, da kuma zabar mutanen da suka cancanta a 2023, domin ba kansu kadai za su zabowa ba, har da ku ma,” in ji ta.

Ta kuma yi kira ga al’umma da su kara ba wa mata gudummawar da ta dace, domin hakan ba iya rayuwarsu zai inganat ba, har ma da tattalin arziki, da zamantakewa da siyasar Najeriya.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos