Ku jira sai Tinubu ya kammala wa’adinsa a 2031 – Shawarar Ganduje ga Atiku da Peter Obi

Ya bukaci su zo don hada kai da Tinubu a yi wa kasa aiki

Ku jira sai Tinubu ya kammala wa’adinsa a 2031 – Shawarar Ganduje ga Atiku da Peter Obi

Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce hukuncin Kotun Koli na tabbatar da nasarar Bola Tinubu a matsayin halastaccen zababben Shugaban Najeriya ’yar manuniya ce cewa zaben ranar 25 ga watan Fabrairu sahihi ne.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Edwin Olofu, ya fitar a ranar Alhamis, Ganduje ya kuma shawarci dan takarar PDP a zaben, Atiku Abubakar da takwaransa na LP, Peter Obi, da su yi hakuri su jira sai 2031, lokacin da Tinubu zai kammala wa’adinsa na biyu.

Tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya kuma taya Shugaba Tinubu murnar yin nasarar, inda ya ce hukuncin ya kawo karshen dukkan wata takaddamar tafka magudi da ’yan adawa ke zargin an yi a zaben.

Ganduje ya kuma ce hukuncin zai ba Tinubu damar mayar da hankali wajen farfado da manufarsa ta farfado da Najeriya wacce jam’iyyarsu ta sa a gaba.

Daga nan sai ya bukaci ’yan takarar da su mayar da wukarsu cikin kube sannan su hada gwiwa da gwamnatin Tinubu wajen kai Najeriya tudun mun tsira.

Shugaban na APC ya kuma roki ’yan Najeriya ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba da su ci gaba da mara wa Tinubu baya har ya kai ga cim ma kudurorinsa na alheri ga kasar.

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro