Ku karbi gaskiya ko daga wa ta fito (1)
Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya ce a cikin littafinSa Mai girma cewa: “An la’ani wadanda suka kafirta daga Bani Isra’il a kan harshen Dawuda da Isa dan Maryama. Wannan kuwa saboda sabon (zunubi) da suke yi, kuma sun kasance suna ta’adi (ketare iyaka), sun kasance ba sa hana juna aikata mummunan aiki, wanda […]
Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya ce a cikin littafinSa Mai girma cewa: “An la’ani wadanda suka kafirta daga Bani Isra’il a kan harshen Dawuda da Isa dan Maryama. Wannan kuwa saboda sabon (zunubi) da suke yi, kuma sun kasance suna ta’adi (ketare iyaka), sun kasance ba sa hana juna aikata mummunan aiki, wanda suka aikata. Hakika, abin da suka kasance suna aikatawa ya munana.” (Ma’ida:78-79).
Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), wanda ya fada a ingantaccen Hadisinsa, cewa: “Ka taimaki dan uwanka, azzalumi ko wanda ake zalunta. Sai sahabbai suka ce: “Ya Manzon Allah, idan an zalunci dan uwanmu mun san ta yadda za mu taimake shi (mu kwato masa hakkinsa), to yaya za mu taimake shi idan shi ne azzalumi?” Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ku hana shi zaluncin, shi ne kun taimake shi.”
’Yan uwa Musulmi! Al’amarin umarni da kyakkyawan aiki da hani daga mummunan aiki, alama ce mai girma daga cikin alamonin Musulunci. Kuma turke ne mai karfi daga turakun al’ummar da ke kan gaskiya. Nassosi masu yawa sun tabbatar da haka, tarihi ya tabbatar da haka, kuma halin da muka tsinci kawunanmu a ciki a yau a kasar nan ya tabbatar da cewa lallai wannan aiki wajibi ne a cikin al’umma.
Al’umma a yau tana bukatar rayar da wannan tafarki na umarni da kyakkyawan aiki da hani daga mummuna, tare da karfafa shi. Domin ta wannan ne kadai za a iya karkade kurar da ta lullube wannan al’umma, kuma ta yi mummunan tasiri a kanta. Sanadiyyar haka sai aka wayi gari ana yi wa wannan al’umma makirci iri-iri, ciki da wajenta. Alhali duk mai hankali ya san cewa ba wani abu ne ya jefa mu cikin wannan hali ba, illa nisan da muka yi daga tafarkin Allah da addininSa.
Umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna, shi ne tsantsar aikin Annabawa da Manzannin Allah. Kai, shi ne ma madarar tafarkinsu. Allah bai aiko Annabawa da Manzanni ba, face su umarci mutane su aikata kyakkyawan aiki, kuma su hana su aikata mummuna. Hadisi ya tabbata (ingantacce) daga Abdullahi dan Mas’ud (Allah Ya kara yardarSa a gare shi), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Farkon abin da ya fara jawo wa Bani Isra’ila kaskanci shi ne: “Mutum zai kasance dan uwansa yana aikata ba daidai ba, yana yin abu maras kyau, idan sun hadu zai yi masa nasiha wane ka ji tsoron Allah ka bar wannan abin ba ya da kyau, haramun ne, shi kuma sai ya ki dainawa. Gobe idan sun hadu, wannan mutum da ya yi masa nasiha zai zauna da shi su ci abinci tare su sha tare, sai Allah Ya jefa kiyayyar juna a zukatansu.” Sannan sai Annabi (SAW) ya ce: “Wallahi ko dai ku yi umarni da kyakkyawa, ku yi hani daga mummuna, ku kama hannun azzalumi ku hana shi zaluncin, ku dora shi a kan gaskiya, ko ku ga abin da ba ku so.”
Duk al’ummar da ta bar wannan aiki na umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna, to ta halaka. A duk lokacin da mutane saboda kwadayi ko tsoro ko kabilanci ko bangaranci ko bambancin addini ya sa suka yi watsi da gwagwarmayar tabbatar da gaskiya da adalci a bayan kasa, to, wallahi sun gama yawo, sai wasu ba su ba, kuma sai buzunsu.
Saboda haka dole ne mu tashi tsaye don ganin cewa al’umma ta koma kan gaskiya, karama da izza sun dawo ga wannan al’umma, daukaka da kwarjini sun dawo ga wannan al’umma. Jagoranci da shugabanci nagari sun dawo ga wannan al’umma, adalci da hadin kai sun dawo ga wannan al’umma, domin samun ci gaba da zaman lafiya a ko’ina. Wannan ba zai taba samuwa ba, dole sai an yi gwagwarmaya domin tabbatar da shugabanci nagari da zai rungumi kowa da kowa bisa daidaito da adalci. Duk yadda ake son al’umma ta gyaru, wallahi idan babu shugabanci nagari ba zai yiwuwa ba.
Ranar 2 ga watan Disamba da muke ciki, tsohon Shugaban kasar na mulkin soja da farar hula, kuma tsohon shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP, Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wata wasika mai tarihi zuwa ga Shugaban kasa mai ci, wato Dokta Goodluck Ebele Jonathan inda ya zargi Jonathan da abubuwa masu yawa da suka hada da nuna sakaci kan harkar tsaro da goyon bayan ta’addanci da ’yan ta’adda da rusa tattalin arziki da bata ci gaban kasa da hadin kan ta da raba kan al’umma da rashin iya mulki da cin hanci da rashawa da nuna kabilanci da kasa cika alkawuran da yayi wa ’yan Najeriya da hada husuma a tsakanin Musulmi da Kirista da sauransu.
Wannan wasika mai shafi 18, kuma tana dauke da kalmomi dubu bakwai da 584. Kuma kafofin watsa labarai na yanar gizo da jaridu da mujallu na gida da waje duk sun buga kwafin wannan wasika ta Obasanjo.
A takaice dai bayan bayyanar wannan wasika, maganganu da rubuce-rubuce sun biyo baya. Kama daga masu goyon baya zuwa masu sukar tsohon Shugaban kasa Obasanjo. Masu goyon bayansa suna yaba masa domin jarunta da gwarzontaka da jajirewarsa a kan fada wa Jonathan gaskiya game da abin da ke tafiya a gwamnatinsa, wanda wannan abu ne a fili da duk dan Najeriya ya san da shi, kuma yake shaida a kansa. Marasa tsoron Allah ne kawai za su yi musu a kan wannan. Wadanda ke sukar Olusegun Obasanjo kuwa, suna ganin bai yi daidai ba da ya bayyana wasikar a kafafen watsa labarai. Sun manta cewa Obasanjo ya bayyana wa duniya cewa, ya rubuta wasika da dama kuma ba alamun gyara. Sannan suna cewa yaushe Obasanjo ya zama mutumin kirki da har zai bayyana laifin wani, ko ya yi wa wani nasiha? Wasu kuwa cewa suke yi, ai duk abin da Jonathan ya yi ba laifin kowa ba ne illa Obansanjo, domin shi ne ya kawo shi.
Imam Murtada Muhammad Gusau (Abu Mus’ab)
Shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Nagazi Okene, Jihar Kogi
08038289761