Ku karbi gaskiya ko daga wa ta fito (2)
A takaice dai, ina son mu sani masu sukar Obasanjo, hujjojinsu ba su da tushe balle makama. Domin babu inda aka ce idan mutum mai laifi ne, ba zai fadi gaskiya a karba ba, ko ba zai yi nasiha ba a kan abin da yake hange na laifi ne ko kuskure. Idan kuwa mun ce […]
A takaice dai, ina son mu sani masu sukar Obasanjo, hujjojinsu ba su da tushe balle makama. Domin babu inda aka ce idan mutum mai laifi ne, ba zai fadi gaskiya a karba ba, ko ba zai yi nasiha ba a kan abin da yake hange na laifi ne ko kuskure. Idan kuwa mun ce haka, to lallai ba wanda zai yi nasiha ko gyara a cikin al’amura, domin Annabawa da Manzanin Allah kadai ne ma’sumai. Kuma duk addinanmu babu inda suka nuna cewa, ba wanda zai yi nasiha sai marar laifi. Abin da addinan suka koyar shi ne, abin da ke kunshe cikin sakon shi za a duba, ba wanda ya zo da sakon ba.
Idan kuwa muka ce dole sai mutum ya kasance marar laifi ko kuskure sannan za a karbi wani bayani ko gyara daga gare shi, to, don Allah daga yau jami’an tsaron Najeriya kada su kara aiki da duk wani bayani da suka tatsa daga bakin mai laifi. Domin muna ganin cewa duk bayanin da suka samu daga bakin mai laifi suna aiki da shi. Kuma idan ma ya kasance duk zargin da Obasanjo ya yi wa Jonathan a wasikarsa, shi Obasanjo ya taba yin irinsa, amma aka kasa samun gwarzon namijin da zai rubuta masa wasika irin wannan don tsoro ko kwadayi, sai kuma ga shi ya rubuta zuwa ga Jonathan, to mene ne laifinsa? Kodai kawai ana so ne a dauke hankalin al’umma daga gaskiyar da ke cikin wasikar Obasanjo a kan gwamnatin Jonathan shi ya sa ake kawo mana wadannan shubuhohi? To ya kamata mu sani, wannan soki burutsun ba zai taba kawar da hankalin al’umma daga wadannan zarge-zarge ba. Domin su jama’a ba wawaye ba ne, suna ji a jikinsu. Kuma ba wanda zai layance su da bayanai na shirme. Gwamnatin Jonathan al’umma sun gaji da ita, canji suke so, suna bukatar shugabanci nagari da zai hada kan ’yan kasa, shugabancin da zai yi wa kowa adalci, kuma ya ba kowa hakkinsa, Musulmi da Kirista da marasa addini.
’Yan Najeriya suna bukatar shugabancin da zai kawo musu zaman lafiya da ci gaba da ’yancin addini da kayayyakin more rayuwa da sauransu.
Ya zama wajibi mu hada kai mu yi aiki tare domin kawar da wannan azzalumar gwamnati mai hada mu fada da junanmu, gwamnatin da ba abin da ta sani sai sata da cin hanci da rashawa da goyon bayan sharri da zalunci. Ya kamata mu sani, idan ba mu kawar da son zuciya ba, to za mu yi da-na-sani.
Wajibi ne mu kalli sakon da ke kunshe a cikin wasikar Obasanjo ba dan sakon ba. Domin a Musulunci, ko Shaidan ya fadi gaskiya wajibi ne mu karbi gaskiyar mu bar shi da shaidancinsa. Hadisin Abu Huraira na Zakkar Fidda-Kai ya tabbatar mana da haka. Kuma wajibi ne goyon bayan mutumin da ya zo da gaskiya, daga duk inda ya fito, ba tare da la’akari da addininsa ko kabilarsa ko yarensa ko bangarensa ba.
A yau, an wayi gari ba wanda zai fada wa Shugaba Jonathan gaskiya face shi da mukarrabansa, sun ce shi dan adawa ne, ko ’yan adawa yake yi wa aiki. kai, ko ma su ce za su zarge shi da laifin cin amanar kasa (treason). To, don Allah ’yan uwana ’yan Najeriya wannan wace irin gwamnati ce da ba ta son gaskiya?
Don haka ya zama wajibi mu yi wa kanmu kiyamullaili, Shugaba Jonathan ya tattara nasa-ya-nasa ya wuce ya bar mana kasarmu ta hade ta zauna lafiya. Mun gaji, Jonathan ya sauka ko ’yan majalisa su tsige shi, ko kuma ya sha kunya a zaben shekarar 2015.
A yau Najeriya ta kasance kamar jirgin ruwa da yake nutsewa a cikin teku, idan mun hada hannu don ceto wannan kasa, mu za mu amfana, idan kuwa mun ki don bambanci na son zuciya, to, mu ne dai za mu ji jiki, kamar yadda muke ji a yau.
Imamu Bukhari da Tirmiziy da Al-Hakim sun ruwaito Hadisi daga Nu’man bin Bashir (R.A) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kwatankwacin mutumin da yake tsaye a kan bin dokakin Allah da wanda yake sabon Allah, kamar wadansu mutane ne da suka zo shiga jirgin ruwa domin su ketare. Kuma jirgin ruwan ya kasance kafin shiga sai an yi kuri’a. Kuma irin jirgin nan ne mai hawa biyu (sama da kasa). Bayan an yi kuri’a, sai wadansu suka samu kasa, wadansu kuwa sama. To, kuma jirgin ya kasance hanya daya yake da shi. Wadanda suke kasa, a duk lokacin da suke so su sha ruwa sai sun bi ta sama. Sai na saman suka fara guna-guni suna cewa, ku fa wadanda ke kasa kuna takura mana a duk lokacin da za ku wuce ku debo ruwa, saboda haka ba zamu sake barinku ku haura ba, don kuna cutar da mu. Sai na kasa suka ce, to tunda kun hana mu, mu kuwa za mu huda jirgin ta kasa don samun ruwan sha, kuma yin hakan zai sa mu daina cutar da ku. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ka ga a nan, idan suka bar su suka huda jirgin nan ta kasansu, ruwa zai cika jirgin ya nutse, kuma za su halaka dukkansu. Amma idan suka hana su, za su tsira, su kubuta baki daya.” Muhammad Nasirudeen Al-Albaniy ya kawo wannan Hadisi a Sahihul Jami’u Hadisi na 5,832 da Silsilatu Ahadisus-Sahiha lambar Hadisi na 69.
Idan kuka tsaya da kyau kuka natsu kuka kalli Najeriya, za ku ga babu bambanci daga yadda Annabi (SAW) ya siffanta wadannan mutane da jirgin ruwa. Idan muka bar Shugaba Goodluck Jonathan ya rusa Najeriya, duk za mu halaka. Amma idan mun hana shi rusa Najeriya, to, za mu tsira gaba daya har da shi. Kuma mu sani, wasikar Olusegun Obasanjo tana da alaka da umarni da kyakkyawan aiki da hani daga mummunan aiki, da Allah Ya umarci al’umma da yi, ko in ce ya wajabta a kan al’umma.
Saboda haka ya zama wajibi ga duk wani mai hankali, mai kaunar Najeriya ya yi murna da wasikar Obasanjo kuma ya jinjina masa a kan wannan namijin kokari na fadar gaskiya komai dacinta.
Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya da rufin asiri da karuwar arziki a wannan kasa tamu Najeriya.
Imam Murtada Muhammad Gusau (Abu Mus’ab)
Shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Nagazi Okene, Jihar Kogi.
08038289761