Ku karkata zuwa ga labarun gargajiya – Amitabh Bachchan

Shahararren dan fim din nan na Indiya, Amitabh Bachchan ya shawarci masu shirya fina-finai na zamani da su koma baya su rika shirya fina-finansu ta amfani da labarun adabin gargajiya, wanda haka zai kara wa fina-finan nasu armashi da amsuwa ga al’ummar duniya.“Na ji dadi kwarai da na ga matasan masu shirya fina-finai a Bengal […]

Ku karkata zuwa ga labarun gargajiya – Amitabh Bachchan

Jarumi Amitabh Bachchan, a yayin da yake kunna kyandir din bude kalankuwar fina-finai ta KolkataShahararren dan fim din nan na Indiya, Amitabh Bachchan ya shawarci masu shirya fina-finai na zamani da su koma baya su rika shirya fina-finansu ta amfani da labarun adabin gargajiya, wanda haka zai kara wa fina-finan nasu armashi da amsuwa ga al’ummar duniya.
“Na ji dadi kwarai da na ga matasan masu shirya fina-finai a Bengal suna nuna hazaka da fitar da fina-finai masu inganci, musamman saboda yadda suka koma baya, suna shirya fina-finan daga labarun kirkira na dauri. Ta haka ne suke samun ingantattun labarai, wanda haka ya kara wa fina-finan nasu armashi da amsuwa a duniya.” Inji jarumi Amitabh, a lokacin da yake bude kalankuwar baje kolin fina-finai mai taken ‘Kolkata International Film Festibal (KIFF).
dan wasan ya kara da cewa, matasan masu shirya fina-finai, ba kawai a Bengal ba, har ma na dukkan fadin Indiya sun fara tattara hankalinsu zuwa ga labarun kirkira na gargajiya. A lokacin da yake ba da misali da marigayi furodusa Rituparno Ghosh, ya ce a lokacin da yake raye, ya kawo canji mai armashi ga fina-finan Bengali, wanda haka ya sanya suka zama rayayyu. Wannan ya nuna irin fikirarsa ta fannin labarun adabin gargajiya.
“Fina-finansa na ‘Chokher Bali’ da ‘Naukadubi’ ya tsara su ne daga labarun dauri na gargajiya, na al’ummar Tagore. Marubutan labarun fim na zamani ma, kamar Suchitra Bhattacharya da Shirshendu Mukherjee su ma sun kasance abin koyi ta wannan fanni.” Inji Amita.
“A shekarun 1980 zuwa 1990, finafinan Bengali sun samu canji sosai ta yadda suka yi tashe a duniya, saboda yadda suka rika amfani da labarun kirkira na gargajiya.” Amita ya kara bayyanawa.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin bikin, Bacchan sai da ya sake burge mutane, inda ya rera wani baitin waka da yaren Bengali.