Ku kashe ni idan na zama azzalumin shugaba- Shugaban Philippines

Shugaban Kasar Philippines, Rodrigo Duterte ya umarce rundunar sojin kasar da ‘yan sanda da su harbe shi idan har ya zama azzalumi kuma ya ci gaba da zama  a matsayin Shugaban Kasa bayan zangon mulkinsa ya kare. Shugaban ya yi wannan bayanin ne bayan wasu daga cikin abokanan hamayyarsa sun fara zargin yiwuwar faruwar hakan, […]

Ku kashe ni idan na zama azzalumin shugaba- Shugaban Philippines

Shugaban Kasar Philippines, Rodrigo Duterte ya umarce rundunar sojin kasar da ‘yan sanda da su harbe shi idan har ya zama azzalumi kuma ya ci gaba da zama  a matsayin Shugaban Kasa bayan zangon mulkinsa ya kare.

Shugaban ya yi wannan bayanin ne bayan wasu daga cikin abokanan hamayyarsa sun fara zargin yiwuwar faruwar hakan, sannan wasu daga cikin magoya bayansa suka fara shirin yi wa kundin tsarin kasar gyaran fuska a majalisa.

Amma shugaban ya kwantar da hankalin mutanen kasar da kuma ‘yan siyasa cewa lallai bai da wannan shirin, sannan ba zai wuce shekarar 2022, lokacin da zangon mulkinsa zai kare.