Ku mayar da hankalinku kan zaben da ke tafe – Abba K. Yusuf

Dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar PDP, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bukaci mutanen jihar su kwantar da hankalinsu, kuma su mayar da hankali kan zaben da ke tafe. Abba Kabir Yusuf ya kuma zargi Jam’iyyar APC da sayen kuri’u ta hanyar rarraba kudi ga masu zabe a lokacin da aka gudanar da zaben […]

Ku mayar da hankalinku kan zaben da ke tafe – Abba K. Yusuf

Abba K. Yusuf

Dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar PDP, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bukaci mutanen jihar su kwantar da hankalinsu, kuma su mayar da hankali kan zaben da ke tafe.

Abba Kabir Yusuf ya kuma zargi Jam’iyyar APC da sayen kuri’u ta hanyar rarraba kudi ga masu zabe a lokacin da aka gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa a ranar Asabar da ta gabata.

Dan takarar Gwamnan wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Yakin neman zaben Shugaban Kasa na PDP a Jihar Kano ya ce Jam’iyyar APC a jihar ta yi nasarar cika burinta ta hanyar sayen ’yancin jama’a, “Mun ga yadda Jam’iyyar APC ta rika raba kudi a rumfunan zabe. Abin ya ba ni mamaki ganin yadda aka yi amfani da talaucin mutane da yunwa da jahilci da ke damun yawancin al’ummarmu aka saye ’yancinsu ta hanyar raba musu kudi da buhunan abinci,” inji shi.

Injiniya Abba ya yi kira ga Hukumar INEC da jami’an tsaro da ’yan jarida a matsayinsu na idanun al’umma su tabbatar sun yi aikinsu yadda ya kamata wajen kare hakki da ’yancin jama’a a lokacin zabe.

Kuma ya yi kira ga ’ya’yan Jam’iyyar PDP su kwantar da hankalinsu tare da mayar da hankali ga zaben Gwamna da na ’yan majalisar dokoki da za a yi, inda ya nemi su yi fitar dango wajen kada kuri’arsu don zaben mutanen da za su shugabance su.