Ku rika daukar nauyin marayu – Sheikh Fasa-Giwa

Wani malamin addinin Musulunci da ke Abuja, Sheikh Haruna Isa Fasa-Giwa, ya hori al’ummar Musulmi su rika daukar nauyin marayu da sauran mabukata da ke cikinsu. Malamin wanda ya bayyana haka a yayin bikin yaye daliban Makarantar Khulafa’ur Rashiduna da ke garin Masaka da ke Jihar Nassarawa, ya ce hakan ya zama dole don samar […]

Ku rika daukar nauyin marayu – Sheikh Fasa-Giwa

Wata daliba ke karvar shaidar saukar karatu a makarantar Khulafa’ur Rashiduna da ke Masaqa

Wani malamin addinin Musulunci da ke Abuja, Sheikh Haruna Isa Fasa-Giwa, ya hori al’ummar Musulmi su rika daukar nauyin marayu da sauran mabukata da ke cikinsu. Malamin wanda ya bayyana haka a yayin bikin yaye daliban Makarantar Khulafa’ur Rashiduna da ke garin Masaka da ke Jihar Nassarawa, ya ce hakan ya zama dole don samar da zaman lafiya da al’umma abar alfahari.

“Za ku iya yin haka ta hanyar biya musu kudin makaranta a lokacin da kuke biyan na ’ya’yanku sannan ku dora su  a kan wata sana’a da samar musu da jarin gudanar da ita don su zama masu dogaro da kansu. Wannan wajibi ne a kan kowace al’umma, ba aiki ne na ganin dama ba,” inji malamin.

Tun farko a jawabin shugaban Makarantar Malam Abubakar Lawan, ya ce makarantar ta Khulafa’ur Rashidun ta fara a shekara ta 2008 a wani gida, yanzu tana gudanar da ayyukanta ne a fili mai girman hekta 1,200  da ke da sashin firamare da sakandare a fannin Islamiyya da boko, sannan an yi mata cikakkiyar rajista da hukuma.

Kimanin dalibai 42 ne aka mika musu takardun shaidar kammala makarantar yayin bikin, wanda ya samu halartar baki daga jihar da kuma yankin Birnin Tarayya Abuja, kumma sarkin Hausawan garin Alhaji Yusuf Umar ne uban taro. Makarantar ta kaddamar da kalanda da ke dauke da hotunan daliban da suka yi sauka a matsayin wani tsari na kara sama mata kudin shiga, inda wanda ya jagoranci kaddamarwar,  Alhaji Abdullahi Gangara ya sayi kwafi 2 a kan Naira dubu 50.