Ku rika jifar magoya bayan APC – Yusuf Agabi

dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Yusuf Muhammed Agabi ya umarci magoya bayan Jam’iyyar PDP a jihar su rika jefar magoya bayan Jam’iyyar APC da duwatsu a duk inda suka tarar da su. Alhaji Yusuf Agabi ya ba da wannan umarni ne a wurin gangamin yakin neman zabensa a garin Obi […]

Ku rika jifar magoya bayan APC – Yusuf Agabi
Ku rika jifar magoya bayan APC – Yusuf Agabi

dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Yusuf Muhammed Agabi ya umarci magoya bayan Jam’iyyar PDP a jihar su rika jefar magoya bayan Jam’iyyar APC da duwatsu a duk inda suka tarar da su.

Alhaji Yusuf Agabi ya ba da wannan umarni ne a wurin gangamin yakin neman zabensa a garin Obi hedikwatar karamar Hukumar Obi da ke jihar a ci gaba da zagayen kamfen din da yake yi a kananan hukumomin jihar.
Alhaji Yusuf Agabi ya ce ta haka ne al’ummar jihar za su nuna bacin ransu ga mummunan
shugabanci da a cewarsa Gwamna Al-Makura ke gudanarwa a jihar. Ya ce “Ina kira gare ku cewa a duk inda kuka ga ’yan APC ku jefe su da duwatsu don lalatattu ne da suka lalata mana kyawawan ayyukan more rayuwa da muka dauki lokuta da dama muna ginawa. Ta haka ne za ku nuna bacin ranku a gare su.”
Ya ci gaba da cewa Gwamna Al-Makura ya durkusar da abubuwan more rayuwa da gwamnatocin PDP da suka shude suka samar wa al’ummar jihar inda ya bukaci al’ummar jihar su kada wa PDP kuri’unsu a
zabubbukan masu zuwa domin kada su sake yin da-na-sani.
A jawabi daraktan kamfen dinsa Sanata Solomon Ewuga ya ce lokaci ya yi da al’ummar jihar da ya kamata su zabi Jam’iyyar PDP a jihar don ceto su daga wahalhalun da suke fuskanta sakamakon
rigirgimun kabilanci da suka ki ci suka ki cinyewa da a cewarsa gwamnatin jihar ke haddasawa.
Ya ce Alhaji Yusuf Agabi ne kawai zai iya ceto su daga halin da suka samu kansu yau kuma ya gudanar da shugabanci nagari.
Abubuwa da aka gudanar a wajen kamfen din sun hada da karbar magoya bayan Jam’iyyar APC sama da 300 da suka canja sheka zuwa PDP da kone tsinsiya don nuna ban-kwanansu da Jam’iyyar APC.