Ku rika kare kanku daga Boko Haram – Sarkin Kano da Atiku

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya bukaci ’yan Najeriya su tashi su kare kansu daga hare-haren ’yan kungiyar Boko Haram.Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin taron addu’o’i na mako-mako a Kano, inda ya ce kada mutane su zaci cewa sojoji kadai za su iya kare su.Ya bukaci malaman addinai su ci […]

Ku rika kare kanku daga Boko Haram – Sarkin Kano da Atiku
Ku rika kare kanku daga Boko Haram – Sarkin Kano da Atiku

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya bukaci ’yan Najeriya su tashi su kare kansu daga hare-haren ’yan kungiyar Boko Haram.
Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin taron addu’o’i na mako-mako a Kano, inda ya ce kada mutane su zaci cewa sojoji kadai za su iya kare su.
Ya bukaci malaman addinai su ci gaba da fadakar da jama’a muhimmancin jaruntaka da juriya, inda ya ce addu’a kadai ba za ta fitar da jama’a daga halin da suke ciki ba sai sun tashi tsaye.
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya ce kada mutane su karaya ganin yadda mayakan Boko Haram ke kwace garuruwa, inda ya ce tilas a al’umma su nuna juriya da sadaukar da rayukansu don kare iyalai da dukiyoyinsu.
Shi ma tsohon Mataimakin Shugaban kasa kuma mai neman tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC, Alhaji Atiku Abubakar ya shawarci jama’a su dauki matakan kare kansu daga mayakan Boko Haram tunda Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen yakar wadannan matsaloli.
Atiku wanda ya  fada wa manema labarai bayan kammala jawabi a wurin bikin  cikar Jami’ar Amurka a Najeriya (AUN) shekara 10 cewa tsaro shi ne babban matsalar da kasar nan take fuskanta.
Ya ce abin bacin rai da bakin ciki ne ganin yadda gwamnati ke sakaci da lamarin tsaro a Arewa maso Gabas. Ya ce kasar nan na da isassun kudin sayo makamai domin yakar ’yan Boko Haram. “Ban amince cewa rashin iya shugabanci ba ne ya hana su daukar mataki sai dai in wani abu ne ya dauke musu hankali. Yakar ’yan bindiga ta gagari gwamnati, gaskiya abin da walakin da kuma daure kai domin gwamnati ta gaza wajen gamawa da tsirarun mutane da ba su wuce kwanaki kadan a gama da su ba, ko sun fi karfin gwamnati ne?,” inji shi.
Ya ce, “Idan gwamnati ko wani mutum ba zai iya kare ka, ba dole ne ka dau matakan kare kai.”