Ku san matan da Tinubu zai nada ministoci

Mata bakwai da ke cikin jerin sunayen ministoci da Shugaba Tinubu ya mika wa majalisa domin tantancewa

Ku san matan da Tinubu zai nada ministoci

Mata bakwai ne Shugaba Tinubu ya mika sunayensu ga majalisa domin tantancewa a cikin jerin ministoci 28 da yake son nadawa.

Kawo yanzu dai babu bayanin ma’aikatun da yake son ba wa rukunin farko na naministocin da suka hada da maza 21 da kuma mata bakwai.

Ga wasu abubuwan da za ku so sani game da matan da shugaban zai nada ministoci:

1- Hannatu Musa

Lauya ce, wadda ta yi digirinta na farko a Jami’ar Buckingham, da kuma digirinta na biyu kuma a fannin shari’a mai da iskar gas a Jami’ar Aberdeen, duk a kasar Birtaniya, inda a halin yanzu take daf da kammala PhD dinta a can.

A watan Yuni Tinubu ya nada ta mai ba shi shawara ta musamman ta fuskar tattalin arziki a fannin al’adu da nishadi.

’Yar asalin Jihar Katsina ce, mahaifar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

2- Iman Suleiman Ibrahim

Tana da shekaru 19 ta kammala digirinta na farko a Jami’ar Abuja, a fannin sanin halayyar dan Adam, kuma yanzu haka Kwamishinar Kasa ce a Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa.

Tsohon shugaban kasa Buhari ya nada ta Darakta-Janar ta hukumar yaki da fataucin bil Adama (NAPTIP) daga shekarar 2020 zuwa 2021.

A 2019, Gwamna Abdullahi Sule ya sanya ta a kwamitin raya tattalin arziki a mahaifarta Jihar Nasarawa.

3- Betta Chimaobim Edu

Likita ce mai shekaru 32, wadda ta kammaala digirinta na farko a Jami’ar Kalaba a 2009, sannan ta je Amurka da Birtaniya inda ta karo ilimi.

A 2019 gwamna Benedict Ayade na jiharta, Kuros Riba ya nada ta kwamishinar lafiya zuwa 2022 bayan da farko ta kasance  mutum mafi karancin shekaru a cikin masu ba shi shawaara.

Kafin nan a shekarar 2013 an nada ta babbar jami’ar lafiya a ma’aikatar lafiya ta jihar.

4- Doris Uzoka Anite

Ita kuma likita wadda daga bisani ta samu kwarewa a fannin nazarin harkokin kudade (CFA), kafin a shekarar 2002 ta jingine aikin likita ta zama Janar-Manaja a bankin Zenith.

A shekarar 2021 ta zama kwamishinar kudi a mahaifarta Jihar Imo, karkashin gwamnatin Hope Uzodinma.

5- Stella Okotete

Tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar ACP kuma har yanzu ita ce Babbar Daraktar Bunkasa Kasuwanci a Bankin Nigeria Export-Import, mukamin da tsohon shugaban kasa Buhari ya nada ta.

Ta kasance mai ba da shawara ta musamman kan muradun karni (MDGs) ga gwamnan Jihar Delta, mahaifarta, daga 2011 zuwa 2015.

Ta yi karatunta na digiri ne a Jami’ar Benson Idahosa da ke Benin, Jihar Edo.

6- Nkiru Onyejeocha

Ta shafe shekaru 12 daga 2007 a matsayin ‘yar majalisar tarayya ce daga Jihar Abia, inda a baya ta kasance tsohuwar kwamishina.

A 2018 ta koma APC daga jam’iyyar PDP, kuma a zamanta a majalisa, wadda maza ke da rinjaye, ta kasance mai rajin ganin jam’iyyu sun ware wa mata wani kaso na kujeru a lokutan zabe.

A 2022 tsohon shugaba Buhari ya karrama ta a matsayin daya daga cikin mata abin koyi ga takwarorinsu a Najeriya.

7- Uju Kennedy-Ohanenye

 

Tsohuwar mai neman takarar shugaban kasa ce a jam’iyyar APC, amma daga bisani ta janye wa Bola Ahmed Tinubu a watan Yunin 2022.

’Yar asalin jihar Anambra ce daga yankin Kudancin Najeriya.

 

Tags