Ku Shirya Wa Aukuwar Ambaliya —NIMET Ga ’Yan Najeriya

NIMET ta ce shekaru 15 ke nan hasashenta na tabbata da kusan kaso 95 cikin 100

Ku Shirya Wa Aukuwar Ambaliya —NIMET Ga ’Yan Najeriya

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NIMET) ta shawarci ’yan Najeriya musamman mazauna Jihar Taraba da yankin Kudu maso Yammacin Najeriya su shirya samun mamakon ruwan sama da ka iya haddasa ambaliya.

Babban Daraktan Hukumar na Kasa, Farfesa Mansur Matazu, ne ya ce sanarwa ta zamo dole, don al’ummar wadannan yankuna su mike tsaye domin tarar ambaliyar tun kafn hakan ta auku.

Yankuna da dama a Najeriya tuni suka fara samun amabliyar, kwanaki kadan bayan faduwar damuna, musamman ma jihohin Legas da Bauchi Kano, in da aka samu asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.

Matazu ya ce tsawon shekaru 15 ke nan hasashen da Hukumar ke yi na tabbata da kusan kaso 95 cikin 100.

A cewarsa dokar tabbatuwar ingancin hasashen yanayi da Hukumar Kula da Yanayi ta Duniya ta fitar shi ne samun tabbatuwarsa da kaso 65 cikin dari.

Haka zalika Daraktan ya koka kan yadda wasu gwamnatocin jihohi da kananan Hukumomi ke watsi da hasashen da Hukumar, inda suke yin abubuwan da za su iya ta’azzara ambaliyar idan ta zo.

Don haka ya yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su dinga ba wa bayanan Hukumar muhimmacin da ya kamata domin rage karfin ambaliya a fadin kasar nan.

Ya kuma bayyana wa Aminiya cewa yanzu haka sun kulla alaka mai kyau da Hukumar Wayar da Kai ta Kasa, hadi da ta yada Labarai, domin shirya bitocin wayar da kai ga masu ruwa da tsaki a kasar, su fahimci muhimmancin hasashen ga rayuwarsu.