Ku shirya wa matsananciyar yunwa a Arewa —Sarkin Zazzau
Sarkin Zazzau ya ce, Idan ’yan Najeriya suna son ingantaccen ilimi, dole ne su biya”
Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli ya ce ko ba a fadawa ’yan Arewa ba, sun san akwai yiwuwar ambaliyar bana da kalubalen tsaro su jefa yankin a halin matsananciyar yunwa.
Sarkin ya bayyana cewa ce lokaci yayi da ya kamata a mike tsaye domi fadada tunanin a bangaren noma.
- Babban Dan tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ya rasu
- Akwai yiwuwar Boris Johnson ya zama Fira Ministan Birtaniya a karo na biyu
“Batun matsalar yunwa a shekara mai zuwa, ba ka bukatar kowa ya yi maka bayani, sai dai addu’ar Allah Ya sa hakan ya zamo zaburarwa ga mutane wajen lalubo wasu hanyoyin samar da abincin.
“Domin mun san Hausawa na cewa sana’a goma maganin mai gasa ce,” in ji Sarkin Zazzau a taron bayar da lambar girmamawa karo na uku da Cibiyar Raya Kasuwanci, Noma da Ma’adanai ta Jihar Kaduna (KADCCIMA) ta shirya.
Ya ce, “Ya kamata mu farka daga barcin da muke yi mu ga me ya kamata mu yi, saboda mun san kashin bayan tattlin arziki a duniya shi ne noma, musamman ma a yankin Arewacin Najeriya.
“Bana noma na cikin mawuyaci hali, saboda ambaliya da kalubalen tsaro”, in ji Sarkin.
Ilimi mai inganci sai an biya —Sarkin Zazzau
Dangane da kukan tsadar da Ilimi ya kara yi a kasar nan kuwa, sarkin ya ce ba a Najeriya ba kadai, a ko’ina ma a duniya ilimin manyan makarantu ba kyauta ba ne.
“Idan ’yan Najeriya suna son ingantaccen ilimi, dole ne su biya. Amma ban ce a tsawwala kudin makaranta ba, don takamar hakan.
“Saboda wasu makarantun, idan ka kwatanta kudin makarantarsu da na makarantun kasashen ketare, za ka ga na wajen sun ma fi arha”, in ji Ahmed Sarki Bamali.
Karshe ya taya wadanda aka karramawar murna, bisa bayar da gudunmawa ga habakar tattalin arzikin Najeriya ta fannoni daban-daban, musamman ma yankin Arewan.