Ku yafe min wahalar da kuka sha lokacin canjin kudi – Buhari

Ya ce da zuciya daya ya kirkiro manufar, ba don a sha wahala ba

Ku yafe min wahalar da kuka sha lokacin canjin kudi – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

A jawabinsa na karshe ga ’yan Najeriya a safiyar Lahadi, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci da su yafe masa wahalar da canjin kudi ta je fa su a kwanakin baya.

Ya ce ya kirkiro manufar ce da zuciya daya, don ya habaka tattalin arzikin Najeriya.

Ya kuma bukaci jama’a da su kara yin takatsantsan sannan su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai don a kawo karshen matsalar tsaro.

Buhari ya ce, “A yunkurinmu na bunkasa tattalin arzikin kasa, mun fito wasu manufofi masu matukar wahala, wadanda galibinsu kwalliya ta biya kudin sabulu. Wasu daga cikinsu sun jefa mutane cikin wahala ta dan wani lokaci, saboda haka ina neman afuwar ’yan uwana ’yan Najeriya, amma da zuciya daya muka kirkire su.

“Sannan a yunkurinmu na tabbatar da samar da isassun ayyukan raya kasa, mun kammala muhimman ayyukan da suka shafe shekara da shekaru, daga cikinsu akwai Dokar Man Fetur, kammala wasu ayyukan lantarki, gadar Neja II da kuma hanyoyi da dama da suke hada birane da Jihohi.

“A fafuktukarmu kuma ta tabbatar da cewa mutane sun zauna lafiya, mun samu muhimman nasarori ta bangaren tsaro.

“Yayin da nake kammala wa’adin mulkina, mun rage yawan ayyukan ’yan bindiga da ta’addanci da fashi da makami da sauran muggan ayyukan laifi.

“Domin dorewar wadannan nasarorin, ina kiran jama’a da su dada sanya idanu sosai ta hanyar taimaka wa jami’an tsaro domin ganin bayan dukkan wata barazanar da take tunkararsu.

“Har yanzu ina zubar da hawaye kan yaranmu da ke hannun ’yan ta’adda, ina jajanta wa iyaye, ’yan uwa da abokan arzikin wadanda ke tsare a hannun ’yan ta’adda bisa zalunci. Dukkan wadanda suke rike, su sha kuruminsu, jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu wajen ceto su ba tare da an cutar da su ba,” in ji shi.

A gobe Litinin ce dai Buhari zai yi bankwana da mulkin Najeriya inda zai mika shi ga Bola Ahmed Tinubu, wanda za a rantsar a matsayin Shugaban Najeriya na 16.

 

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara