Ku yi kiwon zakara domin samun falala- Dakta R/Lemo
Babban Malamin addinin musuluncin nan, Dakta Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo (Allah Ya kara masa lafiya) ya ja hankalin al’ummar musulmi tare da kwadaitar da su a kan su yi kiwon Zakara. Babban Malamin ya yi wannan jan hankali ne a ranar Laraba 11-03-2020 a lokacin da yake gabatar da karatun Littafin “Alwabilussayyib” Littafin da […]
Babban Malamin addinin musuluncin nan, Dakta Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo (Allah Ya kara masa lafiya) ya ja hankalin al’ummar musulmi tare da kwadaitar da su a kan su yi kiwon Zakara.
Babban Malamin ya yi wannan jan hankali ne a ranar Laraba 11-03-2020 a lokacin da yake gabatar da karatun Littafin “Alwabilussayyib” Littafin da yake bayani a kan addu’o’i da Zikirai, a darasin sa na (148) wanda ya saba gabatarwa a dukkan ranakun Laraba bayan Sallar Magriba a Masallacin Cibiyar Imamul Bukhari da ke Rijiyar Zaki cikin Birnin Kano.
A lokacin da Babban Malamin yake tsaka da bayani a kan Hadisin Annabi (S.A.W) wanda Abu Huraira ya rawaito, Al-imamul Bukhari da Muslim suka fitar dashi a cikin ingantattun littafansu, Hadisin da Annabi mai tsira da amincin Allah yake cewa:
“Idan kun ji chara (Kukan) Zakara to ku roki Allah daga FalalarSa, domin ya ga Mala’ika ne.”
A karkashin haka sai Malamin ya ja hankalin al’ummar musulmi, ya kuma kwadaitar dasu a kan su na yin kiwon Zakaru, domin dai idan Zakara ya yi chara yaga Mala’ikun Rahama ne, duk Mutumin da ya yi addu’a a lokacin ana masa fatan amsawa daga Allah, saboda Mala’iku zasu taya shi da cewa: “Ameen.”
Cibiyar Yada Addini ta Almuntadha ce ta fara wallafa bayanin.