Ku zabi shugabannin da za su yi muku adalaci – Sheikh dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi, ya bukaci ’yan daridar Tijjaniyya a kasar nan su fito su zabi ’yan takarar da suke kyautata zaton za su yi musu adalci da kuma gudanar da shugabanci nagari a zaben da za a fara gudanarwa a gobe Asabar. Sheikh dahiru Bauchi ya yi wannan kiran […]

Ku zabi shugabannin da za su yi muku adalaci – Sheikh dahiru Bauchi
Ku zabi shugabannin da za su yi muku adalaci – Sheikh dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi, ya bukaci ’yan daridar Tijjaniyya a kasar nan su fito su zabi ’yan takarar da suke kyautata zaton za su yi musu adalci da kuma gudanar da shugabanci nagari a zaben da za a fara gudanarwa a gobe Asabar.

Sheikh dahiru Bauchi ya yi wannan kiran ne a birnin Minna a taron yi wa kasa addu’ar zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki tare da gudanar da zabe cikin kwaknciyar hankali.
Shehin Malamin wanda Shariff Hassan Maulaya Katsina ya wakilta ya ce bai dace Musulmi musamman ’yan daridar Tijjaniyya su zama ’yan kallo a al’amari irin wannan ba. Ya nuna takaicinsa ganin cewa an yi ta tabka kura-kurai irn wadannan a baya, inda wadanda suka kamata su kasance a sahun gaba a al’amuran siyasa suke komawa baya, alhali da haka za a yi amfani wurin inganta rayuwar wadanda suke wakilta.
Ya tunatar da wadanda ake mika wa amanar shugabanci su rike ta da kyau, domin Allah zai tambayi kowa irin amanar da aka ba a duniya.
Shugaban kungiyar Sautut Tijjaniyya ta Najeriya Malam Musa Ahmad Zarif, ya shaida wa wakilinmu cewa sun shirya taron ne domin su samu matsayar da ’ya’yan kungiyar za su fahimci al’amarin zaben da za a gudanar cikin sauki don taimaka musu wurin rage asarar da za a iya tabkawa da suka hada bata kuri’u yayin zabe.
Shugaban ya ce za su zabi ’yan takaran da suke kyautata zaton za su yi tafiya tare da su ne, ba a yi amfani da su in aka samu nasara a kyale su ba za a sake nemansu ba, sai wa’adin shekara hudu ya kare a waiwaye su. Ya ce, wannan lokacin ya wuce kuma bai kamata su rika sakaci a al’amarin da ya shafi addini da shugabanci ba.