Kudadenmu da aka boye a Biritaniya muke bukata ba hakuri ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba ya bukatar a ba shi hakuri game da kalaman da Firayiministan Biritaniya Dabid Cameron ya yi cewa Najeriya na gaba-gaba cikin kasashen da cin hanci ya yi wa katutu.Shugaba Buhari wanda ke magana a wani taro game da cin hanci a birnin Landana shekaranjiya Laraba, ya ce abin […]

Kudadenmu da aka boye a Biritaniya muke bukata ba hakuri ba – Buhari
Kudadenmu da aka boye a Biritaniya muke bukata ba hakuri ba – Buhari

g Shugaban Qasa Muhammadu Buhari yana jawabi a birnin Landan na qasar Ingilaa shekaranjiya Laraba.	Hoto: Daga Sahara ReportersShugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba ya bukatar a ba shi hakuri game da kalaman da Firayiministan Biritaniya Dabid Cameron ya yi cewa Najeriya na gaba-gaba cikin kasashen da cin hanci ya yi wa katutu.
Shugaba Buhari wanda ke magana a wani taro game da cin hanci a birnin Landana shekaranjiya Laraba, ya ce abin da ke gabansa shi ne a mayar da hankali wajen kwato kudi da kadarorin da barayin gwamnatin Najeriya suka boye a bankunan kasar Biritaniyar.
Mista Cameron ya yi katobarar ce a yayin da yake tattaunawa da Sarauniya Elizabeth ta kasar Ingila, a yayin da yake yi mata bayanin shirin karbar bakuncin kasashen da za su halarci taron koli kan yaki da cin hanci da rashawa da za aka fara gudanarwa a jiya Alhamis a birnin Landan.
Shugaba Buhari ya mayar da martani ne a lokacin da yake jawabi kan yaki da cin hanci da rashawar a sakatariyar ofishin kungiyar kasashe Rainon Ingila, inda ya ce ya yi matukar kaduwa kuma ya ji kunya kan kalaman na Dabid Cameron.
Baya ga Fadar Shugaban kasar, ’yan Najeriya da dama sun caccaki Firayiministan na Birtaniya kan wannan subul da baka, sai dai kuma Shugaba Buhari ya ki sukar Cameron kai-tsaye lokacin da aka tambaye shi game da subul da bakan a wurin taron.
Maimakon haka Buhari ya ce yana fata Ingila za ta taimaka masa wajen kwato dukiyar da barayin gwamnatin Najeriya suka kai kasarta. “Ba zan nemi wani ya ba mu hakuri ba. Abin da nake nema a dawo mana da dukiyar… wannan shi ne abin da nake nema. Me zan yi da ban hakuri? Ina bukatar wani abin kirki ne,” inji Buhari.
Tunda farko Babban Sakataren kungiyar Kwamenwels Mista Baroness Scotland ya ce, kalaman na Mista Cameron ‘abin takaici ne,’ kuma kasa irin Najeriya tana bukatar a tallafa mata ne ba suka ba.
An dai nadi Dabid Cameron ne a faifan bidiyo yana shaida wa Sarauniyar Ingila cewa shugabannin kasashen da suka yi kaurin suna a cin hanci da suka hada da Najeriya da Afghaistan na daga cikin wadanda za su halarci taron yaki da cin rashawa na birnin Landan.
Ba a tantance ko Mista Cameron ya san ana daukarsa a bidiyon ba a lokacin da yake maganar a wani taro da aka yi a fadar Buckingham ta Ingila.
Mista Cameron ya shaida wa Sarauniyar cewa,  “Mun yi wani taron majalisa mai gamsarwa a safiyar Talata, inda muka tattauna kan taronmu na yaki da cin hanci da rashawa. Shugabannin Najeriya za su zo, cikin bakin namu har da shugabannin kasashen da suka yi kaurin suna a cin hanci.”
Ya kara da cewa, “Najeriya da Afghanistan, kasashe ne da za a iya cewa su suka fi kowace kasa matsalar cin hanci d rashawa.”
Kakakin Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi matukar kaduwa da kalaman da Cameron ya yi, inda ya ce watakila Mista Cameron yana magana ne kan kaurin sunan da kasar ta yi kafin Shugaba Buhari yah au mulki.
Jaridar The Guardian da ake bugawa a Ingila ta mayar da martani ga Dabid Cameron kan wannan katobara inda ta rubuta ra’ayin jaridar musamman a kan lamarin tare da bayyana Cameron da wani cikakken munafuki, bayan da ta ce kasar Inigla tana boye wa barayin gwamnatin Najeriya dukiya, sannan kuma Ingila tana dakile duk wani yunkuri da gwamnatin Buhari ke yi wajen ganin an kwato dukiyar da aka sace a Najeriya aka boye a kasar.