Kudancin Kaduna: Allah Sarki, jiya ba yau ba

A makon  jiya da kuma makon  da muke ciki mutanen yankin Kudancin Kaduna da na garin Kaduna sun samu kansu a cikin halin damuwa saboda rikicin da ya faru a garin Kasuwar Magani har ya fara watsuwa a garin Kaduna. A ranar Alhamis din makon jiya ne dai aka samu tashin hankali a garin Kasuwar […]

Kudancin Kaduna: Allah Sarki, jiya ba yau ba
Kudancin Kaduna: Allah Sarki, jiya ba yau ba

A makon  jiya da kuma makon  da muke ciki mutanen yankin Kudancin Kaduna da na garin Kaduna sun samu kansu a cikin halin damuwa saboda rikicin da ya faru a garin Kasuwar Magani har ya fara watsuwa a garin Kaduna.

A ranar Alhamis din makon jiya ne dai aka samu tashin hankali a garin Kasuwar Magani na Karamar Hukumar Kajuru da ke Jihar Kaduna inda Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta ce mutum 55 sun rasa rayukansu, wadansu da dama suka jikkata kuma an yi asarar dukiya mai yawa.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin Kasuwar Magani ya tashi ne a yayin da wani ya yi sata a kasuwar sai aka bi shi ana “Barawo, barawo,” sai ’yan uwansa suka taso domin kare shi, daga nan sai fada ya kaure har lamarin ya kazanta.

Gwamnati na kokarin kwantar da hankali a garin Kasuwar Magani, sai kuma wata fitinar ta tashi a Kujama da ke Karamar Hukumar Chikun, da ke makwabtaka da garin Kasuwar Magani.

Rikicin na Kujama shi ma rahotanni sun nuna cewa ya faru ne a ranar Lahadi, ana cikin cin kasuwar garin sai zuma (kudan zuma) ya tashi, mutane suka kama guje-guje, daga nan zauna-gari-banza suka samu damar tayar da rikici, wanda ya watsu har zuwa garin Kaduna, amma gwamnati ta yi hanzarin sanya dokar hana fita dare da rana domin takaita fitinar, duk da haka an yi wa wadansu barna kuna an kashe wadansu.

Yankin kudancin Kaduna ya fara samun tunzuri ne daga garin Kasuwar Magani a 1980 lokacin mulkin Balarabe Musa, inda kabillun yankin suka bukaci Hausawan da ke garin su tashi su bar musu garinsu. Daga nan ba a sake samun wani munmunan rikici ba sai a 1987 lokacin da wani Rabaran Bako ya yi batacin ga addinin Musulunci. Daga wannan lokacin ne fa yankin Kudancin Kaduna ya yi ban-kwana da kwanciyar hankali, domin ba a dadewa sai wata fitina ta tashi, an yi rikicin Zangon Kataf a 1992, an yi a Kachia da yankin Sanga da garinKafanchan sau da dama, an yi a Zonkwa da sauransu.

Kafin wadannan rikice-rikicen su rika faruwa yankin Kudancin Kaduna yanki ne mai dadin zama da ake gudanar da harkokin arziki iri-iri, akwai manyan kasuwanni da ke ci duk mako da mutane daga ciki da wajen Najeriya suke halarta, kamar Kasuwar Walijo da ke ci ranar Alhamis da Kasuwar Kubacha da ke ci ranar Litinin, wadannan manyan kasuwanni ne da ake hada-hadar citta da sauran kayan amfanin gona.

Kuma a wancan lokacin a Kudancin Kaduna babu garin da ya kai garin Zangon Kataf yawan motocin haya, amma da rikici ya daidaita garin yanzu babu harkoki irin na da a yankin. Shi ya sanya za ka ga babu zirga-zirgar ababen hawa a hanyoyin yankin, musamman daga Kachia zuwa Kwoi.

A garin Zangon Kataf ne aka yi shahararrun attajirai na yankin Kudancin Kaduna wato Alhaji Tankon Kumatu (ATK), mahaifin Alhaji Lawal ATK da Alhaji Yahaya Tanko, tsohon Shugaban Karamar Hukimar Kaduna ta Arewa da kuma Alhaji Mato Zangon Kataf, mahaifin Kwamishinan Kananan Hukumomi na yanzu Farfesa Kabir Mato. A lokacinsu an gudanar da harkokin arziki sosai a yankin Kudancin  Kaduna.

Saboda dimbin cittar da ake samu a yankin ne ya sanya Gwamnatin Jihar Kaduna ta bude kamfanin sarrafa citta a Kachia, har wadansu Turawa sun zo daga kasar waje domin bunkasa masana’antar amma da aka yi wani tashin hankali a gabansu suka ga yadda ak kashe mutane tare da kona dukiyoyi sai suka kwashe kayansu suka bar kasar. Haka al’amarin yake a Karanar Hukumar Sanga inda aka samu ma’adanin nan mai daraja da ake kira “Nikel,” masu zuba jari suna jin tsoron zuwa yankin saboda yawan rikici da ake yi a yankin.

Haka kuma gwamnatin Kaduna ta samo wadanda suka zuba jari a harkar sarrafa dankalin Turawa wanda ya sanya ake kokarin bude wani katafaren kamfanin sarrafa dankalin Turawa a Manchock na Karamar Hukumar Kaura, sai dai kuma ba a sani ba ko masu zuba jarin za su iya daurewa su ci gaba da aikin nasu

Mutane da dama yanzu suna jin tsoron shiga yankin Kudancin Kaduna saboda gudun kada rikici ya rutsa da su, domin rikicin tashi yake yi babu zato babu tsammani. Hakan ya sanya tattalin arzikin yankin ya raunana, shi ya sanya matasan yankin a kullum zuciyarsu a wuya take, da zarar sun ji kyas sai su fara buge-buge da kone-kone.

A shekarun baya mutanen yankin suna zaune lafiya a tsakaninsu, inda za ka ga kabilun yankin suna zaune a gidajen Hausawa suna aiki suka kuma karatun boko, suna auratayya, idan bikin Sallah ya zo tare suke yi, haka kuma idan ana bikin Kirsimati duk tare suke yi. Suna harkokinsu dare da rana babu wata matsala, amma sai ’yan boko suka shiga tsakaninsu, suka cusa masu kiyayyar juna, suka sanya su suna ta kashe junansu, su kuwa suna can a wasu manyan garurruwa suna zaune tare da iyalansu.

Haka kuma kasancewar Kudancin Kaduna yanki ne da yake da sojoji manya da kanana da masu aiki da masu ritaya, hakan ya taimaka wajen ruruta wutar fitina a yankin, domin kuwa sojojin nan, musamman masu ritaya, suna da zafin rai saboda suna ganin duniya ta juya musu baya, ba a damawa da su, don haka ba su da aikin yi sai rura wutar fitina.

Yakamata al’ummomin yankin Kudancin Kaduna su fahimci cewa Allah Ya karrama mutum idan aka wulakanta shi ba za a samu yadda ake so ba. Marigayi Mamman Shata yana cewa “Mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba,” saboda haka babu yadda za a yi a samu ci gaba a yankin Kudancin Kaduna matukar ana kyamar mutane ko kuma ana korar baki, domin ita kasuwa ba ta kyamar kowa, kuma ba zai.yiwu su zauna su kadai ba sai tare da baki.

Bincike ya nuna cewa a duk duniya duk wurin da ya samu ci gaba za a ga cewa baki ne suka taimaka wurin ya bunkasa shi.

Yanzu saboda yawan rikici da ke faruwa a yankin Kudancin Kaduna babu masu sha’awar zuwa yankin su zuba jarinsu domin suna tsorin yin asara, ko ba a jawo masu asara ba akwai karancin mutanen da za a yi harka da su, saboda  yawan barin.yankin da wadansu ke yi. Domin haka ba dabara ba ce a kori mutane a gari, idan babu mutane kango ba zai yi anfanin komai ba.

Ita kuma gwamnati ya kamata ta daure ta rika hukunta masu tayar da fitina, domin rashin yin haka ne ya sanya mabarnata ke samun damar cin karensu babu babbaka.