Kudi ko Iyali

Assalamu alaikum Manyan Gobe tare da fatan alheri kuma da fatan kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin “kudi ko iyali”.Labarin na fadakar da Manyan gobe cewa zumunci ya fi kudi. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi Kudi ko Iyali Malam Sani na da maca daya […]

Kudi ko Iyali
Kudi ko Iyali

Assalamu alaikum Manyan Gobe tare da fatan alheri kuma da fatan kuna cikin koshin

lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin “kudi ko iyali”.Labarin na fadakar da Manyan gobe cewa zumunci ya fi kudi. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi

Kudi ko Iyali

Malam Sani na da maca daya da ’ya’ya biyu. Ya kasance mutum ne mai kwazo wajenaikinsa. A kullum idan ya fita aiki ba ya dawo wa gida da wuri sai da maraice.Abin ba karamin bata wa yaransa rai yake yi ba. Domin, idan ya dawo da daddare a lokacin sun yi bacci haka kuma yana riga su farkawa da safe. Ba su samin ganin mahaifinsu sai ranar Asabar da Lahadi kawai. Duk da hakan ma wataran Lahadin ma yana fita aiki.
Bayan shekara biyar, ya sami lambar yabo a wajen aiki ga karin albashihar da kyautar gida. Iyalansa babu abin da suka rasa walau kayan saka wa ko kayan abinci. Duk da arzikin da ya sa mu,hakan bai sa shi ya rage kwazo a wajen aiki ba.
Rannan matarsa ta ce da shi “Maigida ka hakura da yawan kwazonnan naka mana tun da yanzu babu abin da muka rasa. Ka zauna tare da mu, Kewa tana yi mana yawa idan ba ka nan.” Malam Sani dai duk da maganar da matarsa ta gaya masa bai sa shi ya rage kwazo ba.
Bayan shekara goma, aka ba shi babban matsayi a wajen aiki da kudi mai dinbin yawa. Sai ya gina wa iyalansa gida kusa da teku soboda tsabagen jin dadi. Rannan ’ya’yansa suka ce da shi ya samu rana daya ya zauna tare da su a gida amma aiki ya hana. Rannan bayan ya tafi aiki sai aka yi ambaliya da ta halakar da iyalansa kaf. Saboda yawan aiki, bai san ma abin da ke faruwa a cikin gari ba. Sai a hanyarsa ta zuwa gida ya ga ba zai iya ma gane inda gidansa yake ba saboda ruwa.
Nan ya fashe da kuka yana tuna abin da matarsa take gaya masa na cewa ya hakura da yawan kwazon nan tun da ba abin da suka rasa.
Iyali ya fi kudi Manyan Gobe don haka ka da a fifita samun kudi a kan iyali.