‘Kudi ko Iyali’

Assalamu alaikum Manyan Gobe tare da fatar alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labari mai taken “Kudi ko iyali”. Labarin na koya wa Manyan Gobe mahimmancin rike zumunci a tsakanin juna ya fi na kudi. A sha karatu lafiya.   Malam Sani na da mata […]

‘Kudi ko Iyali’

Assalamu alaikum Manyan Gobe tare da fatar alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labari mai taken “Kudi ko iyali”. Labarin na koya wa Manyan Gobe mahimmancin rike zumunci a tsakanin juna ya fi na kudi. A sha karatu lafiya.

 

Malam Sani na da mata da ’ya’ya biyu. Ya kasance mutum ne mai kwazo wajen aikinsa. A kullum idan ya fita aiki ba ya dawowa gida da wuri sai da maraice. Abin ba karamin bata wa ’ya’yansa rai yake ba. Domin, idan ya dawo da dare lokacin sun yi barci haka kuma yana riga su farkawa da safe. Ba su samun ganin mahaifinsu illa ranar Asabar da Lahadi, ranakun da babu aiki. A hakan ma wata rana kan kasance Lahadin ma ya fita aiki.

Bayan shekara biyar, ya samu lambar yabo a wajen aiki ga karin albashi har da kyautar gida. Iyalansa babu abin da suka rasa walau na kayan sawa ko na kayan abinci. Duk arzikin da ya samu bai sa shi ya rage kwazo a wajen aiki ba.

Ran nan matarsa ta ce da shi “Maigida ka hakura da yawan kwazon nan naka mana tunda yanzu babu abin da muka rasa. Ka tsaya tare da mu. Kewa tana mana yawa idan ba ka nan.”

Malam Sani duk da maganar da matarsa ta fada masa bai sa ya rage kwazo ba.

Bayan shekara goma, aka kara masa babban matsayi a wajen aiki da kudi mai dimbin yawa.  Sai ya gina wa iyalansa gida kusa da teku don tsabagen samun duniya. Ran nan ’ya’yansa suka ce da  shi ya samu rana daya ya zauna tare da su a gida amma tsabagen kwazo bai samu dawowa ba.

Wata rana bayan ya tafi aiki sai aka yi ambaliya ta hallakar da iyalansa  kaf. Tsabagen aiki bai san ma abin da ke faruwa a cikin gari ba. Sai a hanyarsa ta dawowa gida ya kasa gane inda gidansa yake saboda ruwa ya cnye shi.

Nan ya fashe da kuka ya tuna abin da matarsa ke gaya masa cewa ya hakura da yawan kwazon nan tunda ba abin da suka rasa.

Iyali sun fi kudi Manyan Gobe don haka kada a fifita samun kudi a kan iyali.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos