Kudin cinikin mai Naira tiriliyan 3 sun bace – Lamido Sanusi

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Malam Sanusi Lamido Sanusi, ya ce kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) bai shigar da cinikin man fetur na Dala biliyan 20 (kimanin Naira tiriliyan 3 da biliyan 250 gaasusun babban bankin ba.Malam Lamido Sanusi ya bayyana haka ne yayin da ya halarci zaman jin bahasin jama’a da Kwamitin Harkokin Kudi […]

Kudin cinikin mai Naira tiriliyan 3 sun bace – Lamido Sanusi
Kudin cinikin mai Naira tiriliyan 3 sun bace – Lamido Sanusi

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Malam Sanusi Lamido Sanusi, ya ce kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) bai shigar da cinikin man fetur na Dala biliyan 20 (kimanin Naira tiriliyan 3 da biliyan 250 gaasusun babban bankin ba.
Malam Lamido Sanusi ya bayyana haka ne yayin da ya halarci zaman jin bahasin jama’a da Kwamitin Harkokin Kudi na Majalisar Dattawa ya gudanar a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da kwamitin ya ci gaba da zama domin ci gaba da bincike kan zargin bacewar kudin cinikin mai.
Ya ce NNPC ya sayar da danyen mai na Dala biliyan 67 amma ya aike wa Babban Bankin Dala biliyan 47 ne kacal a tsakanin Janairun 2012 zuwa Yulin 2013.
A watan Satumban bara ne Malam Sanusi ya aike wa Shugaban kasa Goodluck Jonathan wata wasika yana zargin Kamfanin NNPC da kin mika cinikin mai na Dala biliyan 50 ga asusun gwamnati. Kuma sakamakon fitowar wasikar fili ne majalisar ta nemi kwamitin ya binciki lamarin.
Sannan lokacin da ya fara bayyana a gaban kwamitin a Disamban bara Sanusi ya ce kudin da ba a sanya a asusun ba sun kai Dala biliyan 12, amma Ministar Kudi Ngozi Okonjo-Iweala ta ce Dala biliyan 10.8 ne. Kuma dukkansu sun ce ba a gama tantance adadin ba, inda kwamitin ya nemi su kammana tantancewar su dawo masa.
Sai dai Kamfani NNPC ya ce kudin da ake zargin sun bace an yi bayanin yadda aka yi da su, kuma kudin da ake cewa ba a sanya a asusun gwamnati ba, an kashe su ne wajen biya tallafin maid a gyara bututun da sauran ayyuka.
Kwamitin wanda ke karkashin Sanata Ahmed Makarfi ya ci gaba da zama a ranar Talatar inda a jawabinsa Lamido Sanusi ya ce akwai bukatar Kamfanin NNPC ya sanar da duniya inda Dala biliyan 20 suka shiga.
Sanata Makarfi ya ce ba kwamitin ko wadanda lamarin ya shafa ne ya kamata su zama masu kara kuma alkalai kan lamarin ba, iyakaci su ba kwamitin hujjoji su kyale hukuncin a hannun Majalisar Dattawa. Kuma ya ba bangarorin da suke takaddamar mako daya su je su daidaita bayanansu su sake bayyana a gabansa ranar Alhamis mai zuwa.
A kwanakin baya rikici ya kaure tsakanin Malam Sanusi da Shugaba Goodluck Jonathan. Hakan ya faru ne bayan Shugaban kasar ya yi zargin cewa Sanusi ne ya tsegunta wasikar da ya rubuta masa inda ya yi ikirarin cewa Kamfanin NNPC bai bayyana yadda ya yi da kusan Dala biliyan 50 na kudin cinikin danyen man da ya sayar ba.
Sai dai Shugaban Kamfanin NNPC Injjiniya Andrew Yakubu ya shaida wa manema labarai bayan dage zaman kwamitin cewa Gwamnan Babban Bankin ya jahilci yadda bangaren man fetur ke gudanar da ayyukansa. Ya ce Babban Bankin aikin banki kawai yake gudanarwa, amma abin da yake yi yanzu aiki ne na masu binciken kudi, shi ya sa yake kalaman da ba su da madogara, lamarin da in da suna da masaniyar al’amuran da suka shafi harkar bangaren man fetur ba za su rika yin haka ba.